Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 10, 2025 at 12:28 PM
YAUSHE ZA KA HUTA ABINKA. ■ Mai aure na cewa: Ina ma dai ma ban yi aure ba. ■ Gwauro/Tuzuru na cewa: Ina ma dai in yi aure in huta. ■ Mai kudi na cewa: Ina ma dai in sami hutun zuciya. ■ Talaka na cewa: Ina ma ni mai kudi ne in huta. ■ Tsoho na cewa: Ina ma dai samartaka ta ta dawo. ■ Babba na cewa: Ina ma dai a ce ni yaro ne, babu wani nauyi a kai na in sha wasa na. ■ Yaro na cewa: Ina ma a ce ni babba ne Rayayye na cewa: Ina ma dai in mutu in huta. ■ Matacce na cewa: Ina ma dai in dawo duniya don in gyara kura-kuraina. Yaushe za ka sami huta ne ya kai Dan Adam? (Saurara ka ji! Da ambaton Allah zuciya take samun nutsuwa) Ra’ad: 28 ~~ Prof. Abdulkadir Ismail
👍 ❤️ 🙏 👏 😢 🥹 38

Comments