
Sirrin rike miji
June 11, 2025 at 06:08 AM
WANNAN HADIN YANA MAGANCE CIWON HAKORI DA HAKORI MAI JINI YAYIN WANKI (BRUSH).
Da farko zaku samo GARIN CINNAMON (girfa) cokali daya kusamu mazubi mai tsafta ku zuba, saiku samo GARIN WURSHI Cokali uku shima ku zuba... (WURSHI wata saiwace da ake magani da ita, ana samunsa gurin masu saida magunguna na gargajiya).
Bayan nan saiku samo GARIN KANINFARI shima ana bukatar cokali daya ko rabin cokali a zuba cikin wadannan garuka da kuka hada, Saiku samo MAN KWAKWA mai kyau shima a zuba cokali uku aciki. Za'asa cokalin aciki a juya sosai ya hade gaba daya.
Bayan an gama hadasu an juya, za'a dinga sanya garin a jikin brush ana goge baki dashi, zai zama kamar shine powder na goge bakin zakuga yana kumfa da kamshi yayin goge baki dashi....
Wannan hadin zai magance muku AMOSANIN BAKI, KOGON HAKORI KO HAKORI MAI JINI in sha Allah.
Yaya Mustyn ku
Mallam Mustee
👍
1