
Sirrin rike miji
June 11, 2025 at 06:10 AM
SOYAYYA TSAKANIN AL'UMMA.
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce:
“Ba ku da cikakken imani har sai kun ƙaunaci juna.”
ولا تؤمنو حتى تحابوا
1. Soyayya wata ƙima ce da daraja da ke cikin zuciyar ɗan Adam wadda Allah ya halitta don ta kasance asalin dangantaka mai kyau a tsakanin mutane.
Duk inda soyayya ta tabbata, to sai zaman lafiya ya bunƙasa, haɗin kai ya ƙaru, da fahimtar juna ta wanzu.
2. Soyayya ita ce ginshiƙin da zamantakewa ke ɗoruwa a kai.
3. Soyayya ita ce ƙaunar da mutum ke yi wa wani ko wasu da zuciya ɗaya, ba tare da ya sa wata manufa ta cutarwa ba. Soyayya na nufin:
Tausayi,
Jinƙai,
Kulawa,
Girmamawa,
Da kuma karɓar juna duk da bambance-bambance.
Akwai nau’o’in soyayya da suka haɗa da:
5. Soyayyar iyali: tsakanin ma’aurata, iyaye da ’ya’ya.
6. Soyayyar zumunta: tsakanin ’yan’uwa da abokai.
7. Soyayyar al’umma: tsakanin ƴan ƙasa ɗaya ko ƙabila ɗaya.
8. Soyayyar ɗan’adam gaba ɗaya: wanda ya wuce iyakar yare da addini , ita ce ta dabi'a.
Idan mutane na ƙaunar juna, zai yi sauƙin warware rikice-rikice ta hanyar tattaunawa ba tare da tashin hankali ba. Soyayya tana sa mutum ya saurari wanda ke da sabani da shi cikin natsuwa.
9. Soyayya tana sa mutum ya damu da halin da ɗan uwansa ke ciki, ta hanyar ba shi taimako, ƙarfafawa da goyon baya. Wannan na rage fushi da kiyayya a cikin al’umma.
10. Ƙarfafa Haƙuri da Juriya
Soyayya tana koya wa mutum ya rinƙa hakuri da jure halin wasu, musamman a lokacin da ya ji ciwo ko kuma aka saba masa. Wannan yana da tasiri wajen hana yaduwar rigima da rikici.
11. . Rage damuwa da Hasala
Idan soyayya ta mamaye zukata, mutane za su daina aikata miyagun ayyuka kamar faɗa,da hassada ,cin mutunci, zagi, ƙiyayya, da yawan korafi – waɗanda ke haddasa zaman dar-dar.
12. Soyayya na taimaka wajen gina al’umma wadda ke kallon juna a matsayin ‘yan’uwa ba tare da bambanci ba. Wannan yana ƙarfafa haɗin kai da jin daɗin rayuwa.
13. Soyayya na aiki da sauƙaƙe fahimta da haɗin kai, komai bambancin harshe ko fahimta a cikin addini.
14. Soyayya ga ƙasa da al’umma na sa mutane su yi ƙoƙari wajen bunƙasa ƙasarsu ta hanyar aiki tukuru da zaman lafiya.
15. Soyayya tana ɗaukar matasa a matsayin ginshiƙai na gaba, ta hanyar horar da su da karantar da su zaman lafiya da haɗin Kai.
Hausawa sun ce: “Soyayya gishirin zumunci ce.”
Wani karin magana na cewa: “Wanda ya ƙaunace ka, ba zai cutar da kai ba.
Misalan Soyayya a Tarihi
A zamanin Manzon Allah (SAW), lokacin da sahabbai ke rayuwa cikin ƙauna, suna rabon abinci da muhalli, hakan ya kawo zaman lafiya a Madina.
A tarihin Hausawa, akwai lokaci da dangantaka ta soyayya da auratayya a tsakanin ƙabilu ta warware matsaloli da dama na yaki da rashin fahimta.
16. Soyayya ita ce ginshiƙin zaman lafiya da haɗin kai. Ita ce gishirin dangantaka, jigon fahimta, da tushen ƙarfafa al’umma. Duk inda soyayya ta wanzu, to rashin jituwa da rikici ba sa samun wuri. Saboda haka, wajibi ne a ɗora gwiwa da gwiwa wajen yada ƙauna da soyayya a cikin gidaje, makarantu, masallatai, da kuma dukan al’amuran yau da kullum.
Shawara: Ya dace hukumomi, malamai da shugabanni su riƙa koyar da jama’a muhimmancin soyayya da gina al’umma mai fahimta da haɗin kai, domin hakan ne zai taimaka wajen kawar da rikice-rikice da nuna bambanci da ya addabi al’umma.
Allah ya sa mu so juna don Allah.
(Daga Madinah)
👍
❤️
4