Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 11, 2025 at 10:52 AM
ABUBUWAN DA SUKE FARANTA WA MATA RAI SU BA SU DARIYA. - Idan tana ‘yar shekara 1, komai yana bata dariya, yana faranta mata rai. - A shekara ta 4 idan manya sun yi tuntube ko sun yi bari yana bata dariya. - A shekara ta 8 zuwa 14 malamanta na bata dariya su sa ta farin ciki, da kuma dukkan wata yarinyar da ba ‘yar ajinta ba, da kuma kalmomi ko maganar da ta kasa furtawa. - A shekara ta 14 zuwa ta 16 nasihar mahaifiyarta na ba ta dariya, da kuma irin kaya da take sawa, da irin kitsonta da kuma yawan nasihar aure da haihuwa. - A shekara ta 17 zuwa 21 kawayenta da ba su damu da kwalisa ba suna bata dariya da kuma rashin wayewar mahaifinta. - A shekara ta 21 zuwa 25 labaran soyayya na sa ta farin ciki, sannan kuma dukkan abin da masoyinta yake so yana faranta mata rai. - A shekara ta 25 zuwa 27 labarun mijinta da kuma abubuwan gwanintarsa na sa ta farin ciki ya ba ta dariya. - A shekara ta 30 ta’alikin da ‘ya’yanta suke yi a kan abubuwa suna bata dariya su sanya mata farin ciki. - A shekara ta 40, yadda wasu mata suke bibiyar abubuwan yayi na bata dariya, duk da cewa ita ma tana kokarin yin hakan. - A shekara 50, tunanin ‘yarta a bisa fahimtar rayuwa na bata dariya, kamar yadda mijin ‘yarta yake faranta mata rai. - A karshe a shekara ta 60 dukkan abin da yake farantawa jikokinta yana faranta mata rai. (Wata ce na ga ta rubuta wannan da Larabci, sai na fassara, Don Allah idan dai haka ne a tabbatar mana ko ma shigar da farin cikin ga iyayenmu mata da ‘ya’yanmu da matanmu da kannenmu, da sauran ‘yan uwanmu mata). ~~ Prof. Abdulkadir Ismail
👍 ❤️ 😂 🙏 11

Comments