Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 11, 2025 at 11:21 AM
🚨 | The Enemy of my friend is my enemy : Taken Fadan Mata. Kar ka bari ka shiga cross fire, wato fadan da ba naka ba. Mata suna da wata dabi'a, kuma ba akan maza kadai take tasiri ba har akan mata yan uwansu. Idan mace na fada da wani, to tana so duk wanda yake tare da ita ya goya mata baya akan wannan fadan, kuma shima ya zama abokin gabar wannan subject din. Wannan kuskure ne. Kuma zata iya saka ka ka bata da mutum, ita kuma shi shirya, kai kuma ya zama sirikinka ko sirikarka. Ku rika wasan buya. Wannan concept din yayi destroying families da yawa, da abokai da yawa da aure da yawa. Kuma daya ne daga cikin dabi'un mutanen jahiliyya. Don kana gaba da wani - shikenan kowa sai ya shiga ya taya ka? Musamman iyayenmu mata. Ka kula sosai, kar don mahaifiyar ka tana fada da matan babanka ta shafa muku, kuma ku rika fada dasu. Duk wannan family feuds din ta haka suke farawa. Enemy of my friend... It has ruined many families Wallahi. Nan wasu mawaka dinnan, wasu twins musicians din nan, matansu suka fara fada har sai da fadan ya raba yan uwan. Twins ne fa, ciki daya suka fito, amma yau gashi sun raba hanya saboda matansu. So kuskure ne babba ka bari matarka ta shiga tsakanin ka da mutane. Wai neighbours ne matansu suke fada, amma mijin daya yana dawo wa shima ya ara ya yafa. Wannan wasan yara ne. Kar ka taba bari mace ta raba ka da wani. Saboda abinda yafi mata sauki fiye da komai shine bayan ta raba ka da kowa sai kaima a wayi gari ta rabu da kai. Shikenan. Malam duk randa ka bari mace ta raba ka da wani, to sai tayi kokarin ta raba ka da Allah da kuma kanka. A duk sanda ka tsinci kanka a cross fire din mata, to abu daya zai fitar da kai: Siyasa da diplomacy. Ka tsaya a tsakiya, kuma don't take things personal. Koda mahaifiyar ka ce kuwa. Kayi mata yadda zata ji dadi sannan kayi kokarin baiwa ko ina hakkinsa. Wannan shine hankali. Allah yasa mu dace. --- Muhammad Ubale Kiru #muhdkiru
👍 🙏 ❤️ 🤔 14

Comments