Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 11, 2025 at 03:19 PM
Matar ka na chan na hawa achaba tana goga cinya da mai machine, hira da mai kifi da mai kayan miya, yawon gulma a unguwa, kana fita ta sa takalmi ta fita yawo, wasu ma yawon Neman asiri da tsafi, gida gida an santa. Hira da karamar murya wa masu shagon unguwa, duk ta saba da mazan unguwa... Baka sani ba... Kana Nan kana zagin mata masu sa hoto ko maza masu sa hoton matansu a FB Alhalin rabin Mazan unguwa babu wanda bai san kalan sha-raban matarka ba saboda zunzurutun yawo a unguwa da Hijabi da daurin kirji.... Baka sani ba... Wasu kuma su zauna da tsiraici a cikin gida maza suyita shigowa ko a jikinsu... Duk samarin unguwa kannenka, abokan kannenka da abokanka sun gama ganin matarka babu riga Babu dankwali, wasu matan ma zunzurutun rashin sanin ciwon kai su dinga bada mama wa yaro a gaban abokan ka da mazan unguwa, wata a kasuwa ma sai ta cire nono wai zata baiwa yaro... Baka sani ba... Wasu matan kuma haka suke yawo masu shagunan unguwa duk sun san warin zufan jikinsu, ba sa wanka sai yawon gulma, mace sai tayi awa a tsaye a shago wai suna magana da mai shop. Wasun ma masu shagunan neh abokanan gulman su. Baka sani ba... Mun san cases dinnan da yawa,, amma ku da yake kuna wuni a office ko kasuwa, bakwa taba sanin abinda matanku suke shuka wa a bayanku, don ana Jin motsinka za a ja wa yara kunne; "Wanda yace wa babanku na fita sai na mishi duka" Kuma wlh in ba randa asiri ya tashi tonuwa ba bazaka taba sani ba. Kuma ana magana har da ire iren matan nan a tsoma Baki..😅 Saboda haka a daidai lokacin da kuke hango laifin wasu, be checking your wives!!! Nobody is a saint; WE ALL SIN, may be differently. Shawara na bada ba wai nace dole ba.💭
👍 😂 🙏 😢 10

Comments