
Sirrin rike miji
June 11, 2025 at 04:15 PM
Mata Dan Allah, sannan Dan Annabi, ku daina roko, roko yana bude muku kofofin barna da yawa a rayuwar ku wanda baku sani ba.
Da roko ana samun nasara a lalata muku rayuwa, wanda har abada an cuceku an gama daku. Akwai maza masu Akidar indai sun bayar suma fa sai an basu.
Sanadiyar roko, Maza da yawa sun rabu da yan' matan su wayanda suke da burin Aura! Ko ni roko ya zama sanadiyar rabuwata da Ex dina.
Yana daya daga cikin abun da nake Alfahari dashi, ga matata, wallahi bata taba rokona ba, koda kuwa katin wayane, Hakan kuma bai hanata kirana da katin ta ba, muyi sama da 1 hour muna waya. Matata bata taba mun flashing ba akan na kirata, idan tana bukatar magana dani, kirana kawai take kai tsaye, Wannan ba karamin daraja da kima ya kara mata a ido naba lokacin da muke soyayya da ita kafin muyi Aure.
Abun dayasa nake wannan Jan hankalinwa Yan' uwa mata shine, shekaran jiya daya daga cikin abokaina yake gaya mun, shekara 2 kenan yana dakon son wata yarinya, ya kasa fada mata.
Na karfafa mishi gwiwa, ya sanar mata, Ashe itama yarinyar tsahon wayannan shekarun itama tana sonshi, fada mishi ne batayi ba. Take suka fahimci junan su, a yadda yaso nan da 5 Months ayi bikinnasu, Amma ta roki ya bari sai nan da shekara guda, ya kuma amince.
Abun mamamki abun takaici, kwana daya da aminta da soyayyar, sai ga request na neman wani abu ya shigo, tana son ya bata wani abu, Amma indirectly akayi tambayar, ya tuntubeni, na kautar da tunanin shi, akan cewa ba wani abu take bukata ba. Sabo da na san baya son roko ko kadan, ba kuma dan bashi da shi bane. Amma halin roko zai iya sawa ya hakura da ita.
Kaso mafi yawa na maza mun tsani roko, musamman idan rokon ya fito ne daga wajan wacca muke son mu Aura. Kwatsam yau, sai ga sako baro baro ya kara zuwa cewa fa, ita wani abu take so a bata. Subhannallah.
Wato a dai dai wannan gabar tana gabar rasa wannan masoyin nata, Mai hankali, tarbiya nutsuwa da kuma wadata dai dai gwargwado, ina da yakinin duk wacca ta sameshi a matsayin mijin Aurenta, tayi dace ta bangarori da yawa.
Yar uwata, idan kin kasance a cikin mata masu roko, duk runtsi kada ki kuskura ki roki wanda kika san kin tsayar a matsayin mijin Aure, ki daure ki cije duk tsananin bukata, alkairin da zaki samu na daguwar darajarki a zuciyar shi, yafi na biyan bukatar da zaki samu idan kin rokeshi.
A matsayin ka na da' namiji ka taba yin masoyiya mai halin roko? Wanne yanayi kake tsintar kanka idan mace ta roke ka musamman wacca zaka Aura? Ka taba rabuwa da masoyiyar ka akan halin roko?
IBRAHIM LAWAN MUSA
👍
🤔
😮
13