Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 11, 2025 at 04:32 PM
ƊANLITI DA BAZAWARA Ta ce masa, "wani dan aiki za ka yi mini, in biya ka dubu biyar." Duk da Danliti bai san matar ba, bai kuma taba ganinta ba, ya ce ya yarda. Wanda ko naira dari ka ce za ka ba shi, zai iya share maka kunci ka sharara masa mari. Ga shi da rufin asiri amma son banza ya yi masa yawa. "Gaban Alkali za mu tafi," in ji matar, "ka ce masa kai mijina ne da ka yi tafiya, shekara uku ba ka gida, yanzu ka dawo ba ka ra'ayina, ka sake ni saki uku. Idan ka yi mini wannan zan ba ka dubu biyar cur!" Da suka tafi gaban Alkali, Danliti ya maimata magana kamar yadda matar nan ta tsara masa. Alkali ya ce, "Na kuwa shaida, matarka ta saku, saki uku." Danliti ya washe baki, wai har ya gama aikin dubu biyar. Ya yunkura zai tashi, sai matar nan ta ce wa Alkali, "Allah ya kyauta aikin Malam, ashe ya kyautu miji ya yi tafiya tsawon shekara uku, bai san ci da shan matarsa ba, kuma ya dawo ya yi mata wannan irin yankan kauna! To, lalle ina karar tsohon mijina da ya biya ni kudin abinci na shekaru uku." Da aka buga lissafi, kudi suka tashi naira dubu dari uku da ashirin. Sai ta ce ya ba ta dubu dari uku, ta rage masa ashirin saboda tsohuwar soyayyar da ke tsakaninsu. Danliti ya hadi yawu kut, idanu suka raina fata, sai zufa, kamar wanda ya hadiye kunama. Ba dama ya ce karya ya yi, Alkali ya sa a daure shi, ko ma a hada masa da bulala. Ya tarkato kudi ya ba matar. Ta zare dubu biyar ta ba Alkali ta ce, "Allah gafarta Malam, akwai bashi na dubu biyar tsakanina da tsohon mijina, ga shi na biya a gabanka." Kwadayi mabudin wahala. Bukar Mada 06/07/2022
😂 👍 😢 🥰 24

Comments