Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 11, 2025 at 04:42 PM
Ba A Aure Saboda Tausayawa. Sai Da Tausayawa Ake Zaman Aure: #tsangayarmalamtonga Maza aka fi samunsu da wannan dabi'ar. Inda namiji zai ce zai auri mace, ko ya auri mace saboda yana tausaya mata. Tabbas tausayawa juna yana cikin jerin abunda ake bukata a samu ga ma'aurata, amma ba zai zama dalilin da masoya zasu auri junansu ba saboda idan shine ya zama dalilin yin auren ana iya samun matsala bayan yin auren. Shi tausayi ko tausayawa ba soyayya bane, shi kuma aure abu na farko da ake bukata wajen masu niyar yinsa ya zama suna son junansu. Wannan yasa idan tausayi yasa kuka yi aure ba soyayya ba, gaba kuna iya samun matsala. Bisa dabi'ar Dan Adam. A duk lokacin da ya maka wani abu saboda tausayi, zai zama tamkar shine yake sama da kai, wannan yasa idan mace ta tausayawa namiji ta aure shi, ba za a samu girmamawan da ya kamata ta yiwa mijinta ba. Haka nan idan namiji ya auri mace saboda ya tausaya mata, ba zai dauke ta a matsayin matarsa na, zai rika mata ganin yar aiki ko kuma ya kasa mata adalci musamman idan ba mai tsoron Allah bane. Duk Wanda aka tausaya masa aka aure shi, zai zama tamkar wanda aka yiwa alfarma, don haka abubuwa dayawa na aure da ya kamata ya samu ko ta samu bazsu samu ba. Mutum bai da izzinin ya saki jiki sai idan wanda ya tausaya yayi, hatta Jima'i sai idan wannan ya nema sannan za a yi. Abun La'akari anan shine, ba ana nufin babu tausayawa ga ma'aurata bane, sai dai ba shine zai zama ginshikin yin auren ba. Nasan wadanda suka samu kansu a irin wannan yanayin zasu fahimce ni. Shi dai aure bayan an samu soyayya juna, a burin zama da juna saboda Allah a matsayin ibada.
👍 🙏 ❤️ 12

Comments