Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 11, 2025 at 08:37 PM
Wani mutum yazo wajen Manzon Allah (ﷺ) yace : Yah Manzon - Rahma zan tambaye ka rayuwar duniya da ta lahira. 1. Yah Manzon Allah ina son in zama mafi sani a cikin mutane ? Sai MANON ALLAH yace "Ka ji tsoron Allah ka bi dokokin Sa. 2. Ina son in zama mafi arziki a cikin mutane ? Manzon Allah ya ce : Ka zama mai wadatar zuci. 3. Ina son na zama Wanda yafi kowa acikin mutane ? Sai ya ce : Ka zama mai amfanarwa. 4. Menene zai kare ni daga wuta ? Sai ya ce : Ka zama mai yawan yin Azumi. 5. Ina so in zama mafi adalci a cikin mutane ? Sai ya ce : Ka so ma d'an uwanka abin da ka ke soma kanka. 6. Ina son in zama mafi amfanin mutane a wajen Allah ? Sai ya ce : Ka yawaita tuna Allah. 7. Ina son imanina ya zama ingantacce ? Sai ya ce : Ka gyara halayen ka. 8. Menene yake huce fushin Allah (SWT.) ? Sai ya ce : Ba da zakka A ɓoye da kyautata wa 'yan uwa. 9. Wani zunubi yafi muni awajen Allah ? Sai ya ce : Mummunar hali shine rowa 10. Ina so in zama mafi biyayya ga Allah ? Sai ya ce Ka bi umurnin Allah za ka zama mafi rinjaye a wurin Allah. Ina roqon Mai karatu dan girman Allah dan son Annabi kayi ƙokari ka tura koda A group 1 ne domin tunasarwa. Manzon Allah (ﷺ) yace : " Idan Allah ya shiryar da mutum guda ta dalilinka, yafi Alkhairi gareka fiye da abaka jajayen raqumma" Allah yabamu ikon yin aiki da abinda mukaji . Ameen 🤲 Abu Ahmad Assiddeeq
🙏 ❤️ 👍 😢 🤲 🥹 22

Comments