
Sirrin rike miji
June 12, 2025 at 04:31 AM
🌅 AZKAR NA TASHI DAGA BACCI
1. Alhamdu lillahil-ladhi ahyana ba'da ma amatana wa ilaihin-nushur
(ٱلْـحَمْدُ لِلَّهِ ٱلَّذِيٓ أَحْيَانَا بَعْدَ مَآ أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ ٱلنُّشُورُ)
“Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya raya mu bayan Ya kashe mu, kuma zuwa gare Shi za mu koma.”
➤ (Sahih al-Bukhari 6312)
2. La ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu wa huwa ‘ala kulli shay’in qadir. Subhanal-lah, walhamdulillah, wa la ilaha illallahu wallahu akbar, wa la hawla wa la quwwata illa billahil-‘aliyyil-‘azim.
➤ Ana karanta wannan don samun lada mai yawa da kariya daga shaidan.
3. Karanta Ayatul Kursiyy (Suratul Baqara: 255)
➤ Domin samun kariya daga sharrin shaidanu da aljanu a rana.
4. Karanta Suratul Ikhlas, Falaq da Nas (3× kowanne)
➤ Don neman tsari daga dukkan sharri da cuta.
5. Shiga bayan gida da addu’a:
“Bismillah. Allahumma inni a‘udhu bika minal-khubthi wal-khaba’ith.”
➤ “Da sunan Allah. Ya Allah, ina neman tsari da kai daga mazannan aljanu maza da mata.”
6. Yin Alwala da Sallah (Raka’a 2 ko fiye)
➤ Idan ka tashi daga barci, yin sallah yana taimaka maka ka fara ranar da albarka da tsari daga sharrin rana.
❤️
👍
😢
🤲
5