
Sirrin rike miji
June 12, 2025 at 04:37 AM
FAHIMTAR JUNA
Allah taa'la Ya siffanta wasu mutane da cewa Basu da ilmi, wasu Kuma basu da hankali, wasu Kuma basu da fahimta.
لا يعلمون ،لا يعقلون ،لا يفقهون
Saboda rayuwa sai da ilmi da hankali da fahimta.
Mafi yawan rikici yana tasowa a cikin al'umma daga masu karancin ilmi, ko ƙarancin fahimta, ko mummunar manufa.
Kowa Yana Magana ne gwargwadon hankalinsa da ilimin sa da fahimtar sa,
FAHIMTA.
Fahimtar juna na nufin iya sauraron juna, fahimtar ra’ayin juna, da karɓar bambance-bambancen juna ba tare da nuna wariya ko ƙyamar juna ba ,( sai idan mutun yazo da wani son zuciya .)
Mutane su fahimci cewa kowane ɗan Adam yana da banbanci da ɗan'uwansa ,Wajan kala, da jinsi,da yanayin halitta, da kuma ra’ayoyi daban-daban ba dole su zama barazana ba, illa ma suna iya kawo cigaba idan an yi amfani da su da hikima.
1. Fahimtar juna na hana tashin hankali da rikice-rikice, domin mutane za su fi sauraron juna da neman mafita cikin lumana.
2. Al’umma za su fi haɗuwa da yin aiki tare idan suna da fahimta da mutunta juna.
3. Fahimta tana koyar da mutane yadda za su girmama ra’ayoyin wasu koda kuwa ba su yi daidai da nasu ba.
4. Lokacin da mutane suka daina rikici kan bambance-bambance, za su fi maida hankali kan cigaba.
Cikin hikima da basira da nuna ƙwarewa da nuna halaye masu kyau, suna taimakawa wajan karɓar gyara.
Rashin yin adalci a wajan ciro maganar wani, Ko mayar martani ga maganar wani,ko bayar da amsa cikin fushi,yakan fusata abokin tattaunawa har yayi fushi yaƙi karɓar gyara.
Kiyayya da ƙyamar juna bisa kabilanci ko addini.ko ƙungiyanci ko ɗariƙanci yana hana karɓar gyara.
Amfani da rikicin addini ko ƙabilanci ko na siyasa Yana rura wutar ƙyama wajan zaman lafiya da fahimtar juna.
Yawaitar labaran ƙarya da jita-jita a kafafen yaɗa labarai wajan kangama soyayya ko ƙiyyaya ga wasu ,ko wani ko wata jama'a, suna hana fahimtar juna da aiki tare.
Hanyoyin Ƙarfafa Fahimtar Juna
1. Ilmantar da jama’a: A koyar da al’umma darajar mutunta juna da zaman tare da juna.
2. Shugabanni su zama jakadu wajan fahimtar juna ta hanyar nuna adalci da kauna ga kowa ba tare da bambanci ba.
3. Fahimtar juna ginshiƙi ne na cigaba da zaman lafiya a kowace al’umma. Idan mutane suna sauraran juna, suna fahimtar bambance-bambancen juna, kuma suna girmama juna, to rayuwa za ta inganta. Kamar yadda wata karin magana ta ce: "Gidan da ake yawan dariya, ba a jin sautin kuka." Wannan yana nuni da cewa fahimta da zaman lafiya na kawo farin ciki da kwanciyar hankali.
Allah ya nuna mana gaskiya ya bamu ikon binta.
❤️
👍
🤲
3