Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 12, 2025 at 06:46 AM
Irin wannan namijin yana da wuyan sha'ani....... Akwai maza guda biyu wanda soyayya bana gaskiya suke yiwa mace ba. 1.yana son ki idan kina masa komai. 2.yana gudun ki idan kin masa wani kuskure koda ace kadan ne zai rabu dake. "" Kinga irin wannan namijin dama ba son gaskiya yake miki ba,duk duniya babu wanda zai ce komai nasa daidai ne dole akwai inda zakayi kuskure,amma karki yarda ki nuna dole komai sai kinyi domin yaci gaba da son ki, ke ma bazaki zama dole daidai sai kinyi ba, akwai inda zakiyi kuskure. "Ki dinga lissafi mutum da zai guje ki saboda kuskuren ki kadan,irin wannan mazan karki aure sa,kar kiyi tunanin zaman aure dashi. Duk mai son ki tsakanin sa da Allah saboda kuskure kadan bazai guje ki ba,in har kika ga namiji ya guje ki to kinyi abu mai muni ne wanda dole zai rabu dake,amma bawai saboda kuskure kadan ba. Haka dabi'ar wasu mazan take. ©️ Nusaiba Tasiu Abdulrahim
👍 🙏 ❤️ 🥹 😢 😮 17

Comments