Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 12, 2025 at 07:14 AM
🚨 Duniya Makaranta: Ka rike sirrinka da kyau. ℹ️ Rubutun da yawa amma akwai fa'ida. Za'a amfana. InshaAllah. Something really motivated me to make this post. Kuyi hakuri bani da rowar ilimi. Duk abinda da nasan zai amfani al'umma musamman matasa na kan yi kokari nayi sharing don kokarin cin Alfarmar Hadithin Manzon Allah SAW cewa abu uku ko ka mutu ladansu baya daina zuwa cikin file din ayyukanka, wanda bada ilmi yana daya daga cikinsu. Malam rayuwa ta lalace. Daya daga cikin munana ayyukan wannan al'ummar shine a yau burin wasu mutanen bai wuce su bi kwakkwafi don su samu labarinka don suyi amfani da shi watarana su cutar da kai. Sometimes sai naji kamar mutane are into the business of sanin sirrin wasu don suyi destroying din su. Tir da wannan hali. Having said that - muyi kokari, mu daure, mu cige, duk surutun ka/ki, duk dokin ka/ki, mu rika controlling bakunan mu akan wane irin information zamu bayar akan rayuwarmu ko rayuwar na kusa da mu. Especially a wajen aiki ko wajen sana'a. Nan ne guri guda biyu da mutane suke sakin jiki suyi sabo har sabon ya zama illa gare su. Shi wajen aiki banzan waje ne. Gurine na competition da hassada. Sannan mutane da yawa fuska biyu garesu. Yanzu masoyinka zai koma makiyinka. Yanzu wata jarrabawa zata zo sai dai kaji suna dorar da bala'i akanka. Kamar dama jira ake wannan lokacin yazo. A yau wajibi ne ka koyi rike sirri saboda majority na mutane da sirrin wasu suke ci. Mata sun fi zama victim na wannan matsalar - Basa iya rike sirrinsu. Shi yasa a yau masu wayo daga cikin mata sun canja strategy. Da suyi sirri da mace gwara suyi da namiji. Shi kuma illarsa shine, yanzu maza suna taking advantage na mata musamman matan aure suna jin sirrikansu don suyi amfani da Vulnerability dinsu suyi iskanci dasu. A chan kin guji surutu ko tonon-asiri, anan kuma kinyi exposing kan ki to sexual exploitation. Haka wajen maganar neman aure. Duk Namijin da yazo sai kin bashi faya faya labaran gidanku. Duk sirrin yan gidanku da naki sai kin fada. Kuma abin haushin shine, ba lalle bane da maganar aure yazo. Haka za kiyi ta raba DVD din rayuwar ki. A karshe kowa yasan labarin ki da rayuwar ki. Have you ever wondered me yasa da mutun ya fara zuwa wajen ki sai ya daina? Garin labarai kika fadi wani abu da ya canja masa raayi. Wai ke Buhari mai gaskiya ko? Be careful, kowa yana da skeleton a wardrobe dinsa. Ke ce mara wayo. So ni a gani na da best approach yanzu shine wajibi ne mu rage magana. Mu rage sharing matsalar mu. Notwithstanding, sunnah ce mai kyau ace yau kana da wani confidant wato ma'abocin rike maka sirri, Manzon Allah SAW ya yi. Yana da ma'abocin sirri wato Hudhayfah ibn al-Yaman. Yana da kyau kafin ka amince da mutum har kayi sharing sirrinka ya zama mutumin kirkine, kuma mutum ne na nesa wanda ba zai iya cutar da kai ba koda yana so. Kuma ya kasance mutum mai addini da tsoron Allah wanda yasan matsayar shari'a akan hukuncin bankada sirri mutane. Ya bani sha'awa da nake wa wata baiwar Allah interview lokacin therapy session. Sai nake cewa ai ke already kina da solutions a hannu kawai kina bukatar push ne. But amma who is your therapist before myself. Tace Malam Muhammad ba wani bane ChatGPT ne. Ta miko min wayarta, ga sessions nan kala kala such as My depression problem, I caught my husband cheating, I m having migraines due to insomnia, How to live in peace with my husband's second wife and so on. So idan kaji cewa you can't trust anyone, ko idan ka fadi sirrinka za'a maka tonon silili sai ka gayawa AI. Although I trust humans more, kuma i seriously discourage putting your life on the hands of a soulness and lifeless entity like AI. Shaikh Omar Suleiman yake cewa, ni Omar bani da abokin sirri, bani da abokin shawara, bani da confidant. Idan naji ina son fadin sirri ko ina neman shawara, ko ina nake, kawai sai nayi alwala, nayi sallah Rakaat biyu, a sujjadata sai na gaya wa Allah sirrina. Idan kuma shawara nake nema sai nace Allah ina neman sha'awar ka, ka bani haske, ka bani ilhama, ka bani wani sign. Yace ko yaga amsa a bacci, ko yana zauna wani yazo gurin yayi magana kamar dan aike, ko kuma kawai yaga abubuwan suna unfolding a gabansa. And I personally find this even more better and more effective. Amma gaskiya sai mai hakuri da tsoron Allah da kuma Iklasi. Shine kadai zai iya amfani da option din nan. I have tried it a few times kuma alhamdulillah. So let's adjust our style. Mu kuma kiyaye magana anyhow. Saboda nan gana wani abu mai mahimmanci zai iya nufo mu, sai hassada tasa wani yayi amfani da past din mu ya cutar da mu don kar mu samu wannan abun. Wani ma don rashin kirki yayanka zai gayawa ko wasu wanda kake jin nauyi. Mutane can do bad things. Sai mu kiyaye. Kai kuma mai bankada sirrin mutane ga Albishir daga Manzon Allah SAW. Yazo a cikin Sunan Al Tirmidhi da Ibn Majah cewa duk me bankada asirin mutane sai Allah ya bankada nasa, ya kunyata shi, har cikin kwaryar gidansa ko dakinsa. --- Muhammad Ubale Kiru #muhdkiru
👍 🙏 ❤️ 🤲 33

Comments