
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
May 15, 2025 at 11:16 AM
*ALLAH YANA DUBI GA ZUƘATA NE.*
-
"Kada ka taɓa yin tunanin cewa Allah yana kallon gangar jikinka ne domin yi maka hisabi akai, a'a yana yin dubi izuwa ga zuciyarka sannan sai yayi maka hisabi akai"
-
"Dukkanin wani aikin da ka aikata, to lallai shi Allah babu ruwansa da wannan aikin komai yawansa, shi dai zai duba zuciyarka ne yaga niyyarka da kuma ƙudrinka na zuci"
-
"Manzon Allah ﷺ, yace: haƙiƙa lallai Allah baya yin kallo izuwa ga gangar jikinku, ko ƙirar ku, (ko fuskokin ku), saidai kaɗai yana yin kallo ne izuwa ga zuƙatan ku"
Sahih Muslim (2564)
-
"Lallai Allah baya yin dubi izuwa ga surar jikinku, ko dukiyoyinku, saidai kaɗai yana yin dubi ne izuwa ga zuƙatan ku da kuma aiyukan ku"
Sahih Muslim (2564)
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
🙏
❤️
👍
4