HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
May 20, 2025 at 10:41 AM
Damuwarka da halin da Musulmi suke ciki na kunci da tashin hankali alama ce daga cikin alamomin Imani. Idan har kuwa ka damu da halin da Musulmi ke ciki: To a halin yanzu da kake karanta rubutun nan yan uwa a zirin Gazza na cikin tashin hankali irin wanda ba zai siffantu ba. Ruwan bama bamai Isra'ila take zuba musu ta ko ina tana kisa babu babba babu yaro. Dayawa sun mutu da yunwa da kishin ruwa, saura da suke jiran layin nasu mutuwan suma tana zuba musu mahaukacin wuta tana konesu..... Wannan kenan a takaicen takaitawa. Me yakamata muyi? 1) Addu'a 2) Taimakonsu da abinda zamu iya na kudi domin su samu suci dan abinda yake samuwa da mahaukacin farashi mai tsada 3)Kai ma kayi rubutu a shafinka akansu, ko kake sharing idan ka gani saboda ka zama sanadiyyar ankarar da sauran yan uwanka Musulmi.
😢 🙏 😭 ❤️ 👍 23

Comments