
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
May 22, 2025 at 10:40 AM
DABBAR LAYYA.
-
Wacce dabba ce tafi falala a wajen yin layya, ƙatuwa mai nama sosai da maiƙo, ko kuma wadda tafi tsada?.
-
"Sheikh Uthaimin R.A yace: Idan mukayi duba izuwa ga amfanin yin layya, za mu fahimci cewa mai nama sosai tafi falala, duba da kuma gasgatuwar ibadah ga Allah, wadda tafi tsada za tafi falala, amma dai mutum yayi abinda yaji ya fi kwanta masa a zuciya, idan kaga cewa yinta zai ƙara maka imani da ƙasƙanta kai ga Allah, to gwara kayi hakan"
مجموع الفتاوى.
-
"Duk wata ibada wacce Allah ta'ala ya shar'antawa bayinsa, to haƙiƙa yayita bisa tsari da ƙa'idah ta yadda duk wanda ya saɓa wannan tsari ko ƙa'idar, to lallai ibadarsa tana cikin garari"
-
"Kada kayi tunanin za kayi gaban kanka a wata ibadah komai ƙan-ƙantarta sannan kace Allah zai karɓa daga gareka. Burin kowane mai ibadah shi ne Allah ya amsa daga gareshi, to lallai muddin bakabi yadda akace ba, to haƙiƙa baza a karɓa gada gareka ba"
-
WhatsApp channel
https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6
👍
🙏
❤
❤️
9