
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
May 27, 2025 at 04:53 AM
WA ZA KAYI ABOTA DA SHI?.
-
"Kada ka yarda kayi kuskuren karɓar kowa a matsayin aboki a rayuwarka face sai wanda zai kusanta ka ga Allah maɗaukakin sarki. Lallai ka sani! Abokanai sukanyi matuƙar tasiri wajen gyaruwar tarbiyyar mutum ko kuma gurɓacewarta"
-
"Idan kayi sa'ar samun abokanai nagari, sai kaga suna jiyar dakai tsoron Allah kuma suna hanaka saɓa masa, amma idan baka yi dace ba, sai kaga ka haɗu da mugwaye waɗanda zasu dinga ziga ka kana saɓawa Allah. Sabida haka ka tsaya kayi nazari kuma ka tantance kafin ka ƙulla abota da mutane, tabbas ba kowa ne mutumin kirki ba, amma kuma akwai mutanen kirki da yawa sai dai kuma samun su ne wani lokacin yakan yi matuƙar wahala"
-
"Wasu abokanan babu ruwansu da inganta alaƙar ka da Allah, babu ruwansu da cewa kaji tsoron Allah, su kawai burinsu ka biye musu a cikin dukkanin sha'anin su mai kyau ne shi ko mara kyau"
-
"Kada kayi abota da mutanen banza, domin da sannu za su dinga rinjayarka har sai sun ga ka zamto halinka ya koma irin nasu, lallai ne, abokanai suna da matuƙar tasiri a wajen lalacewar mutum ko kuma gyaruwarsa"
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
❤️
👍
🙏
🥹
4