HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
May 27, 2025 at 07:03 AM
GOMAN ZIL-HIJJAH. - "Kamar yadda kake matuƙar ƙoƙari da dagewa wajen ganin ka tsananta ibada da aiyukan alkhairi a goman ƙarshen Ramadana, to haka ya kamata ka tsananta wajen aikata aiyukan alkhairi a cikin goman farkon zul-hijjah" - "Ranakun farkon goman zul-hijjah ranaku ne masu matuƙar tarin falala a cikinsu, a cikinsu akwai ranar Arafah wacce Allah yake yawaita ƴan'ta bayinsa a cikinta" - Ibn Uthaimeen r.h yace: Goman zil-hijjah tana farawa ne daga shigar watan zul-hijjah. ta kuma ƙare da shigar ranar idin layya... Abin mamaki! Lallai mutane suna gafala daga waɗannan kwanakin, zaka samesu a goman ƙarshen Ramadan suna masu matuƙar ƙoƙari, amma a goman zul-hijjah zaka sami wani ma baya bambance tsakaninsu (goman farkon zul-hijjah) da wasunsu ma. اللقاء الشهري (63) - WhatsApp channel https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i - Telegram channel https://t.me/hausaislamicpicturesquotes - Biyo Instagram ɗinmu https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6
🙏 1

Comments