HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
May 27, 2025 at 07:10 AM
HUKUNCE HUKUNCEN LAYYA A TAƘAICE. - An sharɗanta ga raƙuma da shanu, awaki da tumakin da za ayi layya dasu; cewa su kasance sun kuɓuta daga aibukan da za su sanya naman dabbobin ya ƙaranta; don haka; yanƙwananniyar dabba ba ta isarwa, haka kuma karyayyiya, da mai ido ɗaya, da maras lafiya. - ANA RABA NAMAN LAYYA GIDA UKU. - ▪️Ana ci daga gareta. ▪️Ana bada kyautarta. ▪️Ana bada sadaƙarta. - SHARUƊAN LAYYA. - ▪️Musulunci. Layyah ba ta inganta idan wanda ba musulmi ba ya aikata ta. Musulmi shi ne layya take halatta a gareshi. - ▪️Balaga da hankali. Duk mutumin da bai kasance baligi mai hankali ba, ba a kallafa masa yin layyah ba. - ▪️Samun iko da dama. Wannan ikon na tabbatuwa idan mutum ya mallaki ƙimar da zai sayi abun layya dashi, bayan ya mallaki abincinsa da na iyalansa, na tsawon ranar idi. - WhatsApp channel https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i - Telegram channel https://t.me/hausaislamicpicturesquotes - Biyo Instagram ɗinmu https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6
👍 🙏 3

Comments