
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
May 27, 2025 at 06:50 PM
KᗩᗷᗷᗩᖇOᖇI ᗩ GOᗰᗩᑎ ᖴᗩᖇKOᑎ DHUᒪ-ᕼIᒍᒍᗩᕼ.
-
ᴋᴀʙʙᴀʀᴏʀɪ ꜱᴜɴ ᴋᴀꜱᴜ ʙɪʏᴜ:
𝙈𝙐𝘿𝙇𝘼𝙆.
𝙈𝙐𝙆𝘼𝙔𝙔𝘼𝘿.
-
𝐌𝐔𝐃𝐋𝐀𝐊: Itace kabbarar da ba'a ƙayyade ta da komai ba, an sunnanta ta a koda yaushe, acikin safiya da maraice, kafin sallah da kuma bayan sallah, kai acikin kowane lokaci ma.
-
𝐌𝐔𝐊𝐀𝐘𝐘𝐀𝐃: Itace kabbarar da aka ƙayyade yinta a bayan salloli.
-
An sunnanta yin kabbara muɗlaƙ daga kisfewar rana ta ƙarshe acikin watan zul-ƙa'adah har izuwa kisfewar rana ta goma shi uku (13) na watan zul-hijjah.
-
Amma kabbara muƙayyad, ana farawa ne daga asubar ranar arfah izuwa kisfewar ranar sha uku ga watan zul-hijjah (ayyam at-Tashreeq), gameda sha'anin kabbara muɗlaƙ, da zarar mutum yayi sallama daga sallarsa ta farillah, yayi istigfãri sau uku, yace Allahumma antas-salam... izuwa ƙarshenta, sai ya fara yin wannan kabbarar.
-
Wannan banda mai aikin hajji, amma shi wanda yake aikin hajji zai yi kabbara muƙayyad ne cikin haƙƙinsa daga azahar ɗin ranar yanka.
-
شيخ محمد صلاح المنجد حفظه الله.
-
Don Allah kada ka datse mana komai daga cikin rubutun nan.🙏
-
WhatsApp Channel
https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i
❤️
👍
2