HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
May 28, 2025 at 10:59 AM
AMBATON ALLAH ACIKIN GOMAN FARKON DHUL-HIJJAH. - "Akwai wasu zikirori waɗanda akanso su zamto ɗabi'un ɗan adam musulmi a koda yaushe na rayuwarsa, amma anso yafi zage damtse wajen ƙoƙarin yinsu musamman acikin kwanaki goman farkon irin wannan watan na zil-hijjah" - Wato sune hailala, da kabbara, da kuma hamdala. - 𝗛𝗔𝗜𝗟𝗔𝗟𝗔: itace yawaita faɗin La'ilaha ilLalLah. - 𝗞𝗔𝗕𝗕𝗔𝗥𝗔: Itace yawaita faɗin Allahu Akbar Allahu Akbar. - 𝗛𝗔𝗠𝗗𝗔𝗟𝗔: Itace yawaita faɗin Alhamdulillah. - A dunƙule kuma, sai kace: ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA'ILAHA ILLALLAH, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD. - "An sami ruwaya daga Bin Umar Allah ya ƙara masa yarda yace, lallai Manzon Allah ﷺ, yace: haƙiƙa babu wasu kwanaki mafi girma a gurin Allah buwayi, kuma waɗanda aiki a cikinsu yafi soyuwa a gurinsa fiyeda waɗannan kwanaki goman (na farkon watan zul-hijjah) to ku yawaita yin hailala, da kabbara, da hamdala acikinsu" {رواه الطبراني في المعجم الكبير} - WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i
❤️ 🙏 👍 6

Comments