HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
June 2, 2025 at 02:25 PM
*SHARUƊAN INGANCIN LAYYA*
-
"Layya tana da sharuɗa waɗanda idan ba'a cikasu ba, to lallai wannan layyar bata da inganci balle a karɓeta a bawa ma'abocinta lada, ga wasu daga ciki;
-
💧"Abinda za'ayi layyar su kasance daga cikin jinsin dabbobin ni'ima ne, kamar rago, bunsuru, saniya, raƙumi"
-
💧"Su kuɓuta daga aibu, kamar makanta, gurguntaka, karyewar ƙaho ko jela, kodai yankewar wani sashin jikinsu, kamar tsagewar kunne, da yankewarsa"
Sunan Nasa'i : (4372)
-
💧"Sannan kuma sukai ƙimar shekarun da shari'a ta tanadar musu, shekara ɗaya ga rago, biyu ga akuya, biyu ga saniya, biyar kuma ga raƙumi"
Zadul ma'ad, (2/317)
-
"Waɗannan wasu ne daga cikin sharuɗan da za'a cika domin a tabbatar da ingantacciyar layya, ya Allah ka larɓa daga garemu"
-
-
WhatsApp Channel
https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i
❤️
❤
👍
🙏
🤲
6