
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
June 4, 2025 at 02:10 PM
*FALALAR AZUMIN RANAR ARFA*
-
Manzon Allah (SAW) ya sunnanta yin azumin
ranar arfa wato ranar tara ga watan
zulhijja ga wanda bai je aikin hajji ba domin suma suyi tarayya da
wadanda Allah ya ba su ikon zuwa ta
wajen samun lada da kuma alkhairan
dake cikin wannan rana mai albarka
ta Arfa.
-
Manzon Allah (SAW) yace: " Azumin
Arfa ina tsammani Allah Ta'ala zai
kankare da shi zunuban shekarar
dake gabaninsa da wacce take
bayansa".
Muslim.
-
Telegram
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Instagram
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5