
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
June 10, 2025 at 04:22 AM
ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE.
-
"Kada ka rafkana daga zikirori a rayuwarka, musamman ma irin zikirorin safiya da maraice, da makamantansu, domin haƙiƙa shaiɗan yakanyi galaba kan duk wanda yake gafala daga yin addu'oi a rayuwarsa"
-
"Sau nawa wata musiba take shirin afkuwa gareka amma a dalilin addu'oin da ka kasance kana yi yau da kullum sai Allah ta'ala ya karkatar da wannan musibar izuwa wani gurin, sau nawa wani bala'in yake tunkaroka amma dalilin zikirorin da ka kasance kana yi sai Allah ya taƙaita wannan bala'i ya sauka a kan kayanka a maimakon ya sauka a karan-kanka"
-
"Haƙiƙa akwai falala a cikin yin zikirori a rayuwa, domin haƙiƙa shi zikiri kariya ne kuma garkuwa ne ga bawa, sannan kuma haƙiƙa Allah yana bawa bawansa lada idan ya kasance yana kiyaye yin zikiri musamman irin zikirin da ya tabbata a sunnah"
-
❝Duk wanda yace SubhanAllahi Wa bi Hamdi سبحان الله وبحمده Sau ɗari a rana, za a kankare masa zunubansa koda kuwa sun kai misalin yawan kumfar kogi❞
-
WhatsApp Channel
https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i
❤️
❤
5