
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
June 12, 2025 at 06:54 AM
DA'AWA SAI DA HAƘURI.
-
"Idan ka kasance mai yin da'awa ne (kira zuwa ga Allah) to dole sai ka kasance mai yin haƙuri da mutane da kuma kawar da kai daga wautarsu, kuma sai ka dage ka jure"
-
"Ƙosawa ko gajiyawa ba naka bane, domin lallai shiriya ba a hanunka take ba, a hanun Allah take. Kada kaji haushi don mutane basu fahimceka ba, sannan kuma kada ka zamto marar haƙuri a ɓangaren kira ga addinin Allah"
-
Mallam Assa'idiy (r.h) yake cewa: "Kayi haƙuri dangane da kiranka ga mutanenka, haƙuri mai kyau, kada ka ƙosa ko ka gajiya, ka cigaba da bin umarnin Allah, ka kirayi bayinsa a kan kaɗaitashi, kada ƙin yimaka biyayya yasa ka daina, ko rashin kwaɗayinsu ga addinin, domin a cikin yin haƙuri a kan hakan akwai alkhairi mai yawa"
-
WhatsApp channel
https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6

❤️
👍
🙏
3