
HAUSA ISLAMIC PICTURES QUOTES
June 12, 2025 at 10:27 AM
*KI ZAMTO MAI HAƘURI A RAYUWARKI.*
-
"Kada ki kasance mai yawan damuwa abisa abinda zai ke fitowa daga bakunan mutane game dake, idan kin kasance ɗalibar ilmi mai riƙo da addininki, mutane zasu dinga faɗar munanan maganganu akanki marasa daɗi"
-
"Zasu dinga faɗin cewa kina da girman kai, ko ke baki waye ba, da dai sauran munanan maganganu masu ɗigunzumarwa, to amma kada ki damu, ki mayar da dukkanin ilahirin lamuranki zuwa ga Allah, zaki sami sauƙin lamarinki"
-
"Mutane zasu kutsa cikin rayuwarki, zasu dinga yin ƙoƙarin suga sun zaƙulo wani aibu a tattare dake, zasu dinga jefa mummunan ƙazafi acikin rayuwarki, amma idan kika kasance mai kamun kai, kika yi haƙuri abisa duk abinda mutane za suce game dake, kika gyara tsakanin ki da Allah, sai Allah ya kawo miki sauƙi acikin rayuwarki"
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
❤️
❤
👍
6