
โฆโง ๐๐ ๐ช๐๐๐ฏ ๐๐๐๐๐๐๐ โงโฆ
May 25, 2025 at 09:25 AM
Crypto = Strategy
________/________
From Zero to Profits: Wato wannan shine Strategy mai aiki ko kuma nace wanda yake fita. Kafin hakan dole kana buฦatar abubuwa guda biyarโIndai kana da waฦดennan abubuwan to in shaa Allahu dole sai ka fara samun kuษi ko nace riba a Crypto Trading ษin da kakeyi.
1]-Abu na farko dai shine (Educate Yourself), bro/sis babu shortcut a wannan bangaren. Indai kana son ka samu kuษi a Crypto ko ka iya trading, ya zama dole sai ka fara gina kanka da ilimi. Wlh duk kuษinka idan babu ilimi zaka daษe kana buga-buga a kasuwar crypto tare da yin asara mara dalili.
Dan haka, abu mafi mahimmanci da yakamata kowa ya sani kamar yadda kusan kowa ษin ya sani shine ya zama dole ya mutum ya nemi ilimi kafin investing a crypto idan kana son samun zaman lafiyar dukiya da kuma samun kwanciyar hankalinka. Ilimi yana matukar taka rawar gani a wannan space ษin. Space dama da masu ilimi suke wasa da hankalin jahilai.
2]-Abu na biyu shine (Concrete Goals), wato ya zama dole sai ka samarwa kanka wani Clear Goals da zaka tabbata a kansa. Domin Emotion ษinka shine kusan yake jagorantar 80%-90% ษin duk wani yanke hukuncinka a crypto. Dan haka 'You must set a clear Goals' idan kana son kayi trade successfully a crypto.
3]-Abu na uku shine (Trading Plan), duk wani Successful Trader da ka sani a duniya to dole akwai wani Trading Plan da yake dashi. Wannan abu ne da kowa yake da irin nasa, dan haka kaima ka samarwa da kanka naka. Misali: Kamar ni, a sati akwai iya ranaku da lokacin dana ware gurin yin Trading ษina a baya. Sannan ba ko wanne lokaci nake shiga Trade ba koda kasuwar babu Volatility sosai.
Da yawan lokaci nafi shiga Trade cikin dare zuwa wayewar gari. Idan ina son nayi Trade akan wani Token/Coin a baya, so adding ษinsa zuwa Fav Section ษina ne, sai nayi 'Volume Analysis' akansa zuwa wani ษan lokaci kafin na shiga. Idan naga ana samun demand either massive or small, to sai nayi amfani da Trading Plan ษina na yanke hukunci. Dan haka kaima yakamata ka koyi hakan.
4]-Abu na huษu shine (Demo Account), ษan uwa da shawara kake nema sai nace ma ka fara koyar Trading da Demo kafin ka fara zuba kuษinka. DEMO ACCOUNT, free money ne da aka tsara za'ai Trade dasu aci riba ko a faษi dasu amma ba tare da ka ita cire kuษin ko riba ba. Da yawan wasu Exchanges ษin sukan bawa new users ษinsu irin wannan demo account ษin domin ilimantarwa. Kamar wani practical ne da akeyi da kuษin bogi, bawai real money bane domin gujewa asara.
5]-P2P = Real Profits! Wato malam abu mafi mahimmanci da yakamata ka dinga yi shine a duk lokacin daka samu kuษi a Crypto, to ka tabbatar da kacire abunda ka samu idan kana da bukata. Koda kaci riba a Crypto Market, bata tabbata taka ba sai lokacin da kayi p2p kaga saukar kuษin a account ษinka. Domin sau da yawan lokaci idan mutum yayi wani (Successful Trading) ษin daya samu Profits sosai, emotion ษinsa yana iya sake yaudararsa domin sake shiga wani Trade ษin nan take domin ฦara samun wani Profit ษin, wanda hakan yakan iya janyo mutum ya rasa capital tare da Profits ษinsa gaba ษaya.
Dan haka, taking profit is one of the best Strategy dana yi imani dashi a harkar Crypto Currency. Ba'a na damar taking profits sama da yadda ake na damar rashin taking profit ษin a Crypto. Dan haka, ya zama dole kayi aiki da wannan Strategy ษin idan kana son ka amfana da wani abun a wannan space ษin. In shaa Allahu nan gaba zamu sake baku wasu shawarorin da muke tunanin zasu amfanar daku game da crypto trading. Abunda muke faษa muna faษin sune 'By Experience', dan haka yana da kyau a matsayinka na sabon Trader ko mai son fara Crypto Trading kayi aiki dasu.
Allah ubangiji yasa mudace.
#aminudayyibzakariyya