
✦✧ 𝐀𝐃 𝗪𝗘𝗕𝟯 𝐀𝐂𝐀𝐃𝐄𝐌𝐘 ✧✦
June 13, 2025 at 01:18 AM
Notcoin, Not Pixel, da Waɗanda sukayi Void an raba musu stickers daga team ɗin Notcoin, wanda ana shirin fara pre-market ɗin su kamar yadda aka fara pre-market ɗin Notcoin voucher.
Sai dai ba random suka raba ba. Akwai matakai da dole ne ka cimma kafin a baka sticker na wannan matakin. Zaka iya samun fiye da ɗaya, gwargwadon matakin da ka kai.
Waɗanda sukayi Notcoin an basu sticker da ke daidai da level ɗinka: diamond league, bronze, da makamantansu. Ku duba wajen inventory.
Waɗanda sukayi Notpixel an raba musu pixel dudes da leader. Su ma duba wajen inventory.
Waɗanda suke Void, suma an basu stickers guda 7 — ko kuma ya danganta da yadda aka raba lokacin da muka gama Season 0. Duba inventory.
Wajen achievement kuma, an bada stickers 2:
Test Pilot: An baiwa waɗanda sukayi aiki tukuru tun daga lokacin testnet na Notcoin.
Alpha: An baiwa waɗanda suka kawo community lokacin Notcoin.
Notpixel:
Alliance: Idan ka gayyato mutane 128.
King: Idan ka gayyato sama da mutane 1000.
Void:
Idan ka kasance cikin waɗanda suka samu sticker lokacin da aka gama Season 0, sai aka baka Zero Champion. Iya mutum 2500 suka samu wannan sticker
Wannan shine airdrop na farko da TON Blockchain ta bayar ta hanyar stickers, a kokarinsu na farfaɗo da kasuwar NFT da akeyi a Blockchain ɗinsu.
Duk da haka, yanzu haka su ne Blockchain da yafi samun karbuwa da kuma bada riba a kasuwancin NFT.
Zaku iya duba sticker nawa suka ba ku a nan:
🔗 https://t.me/notgames_bot/profile
(ba referral link bane)
An kusa buɗe pre-market domin fara cin kasuwa. Ubangiji Allah ya bamu sa'a, yasa suyi daraja.