✦✧ 𝐀𝐃 π—ͺπ—˜π—•πŸ― π€π‚π€πƒπ„πŒπ˜ ✧✦
✦✧ 𝐀𝐃 π—ͺπ—˜π—•πŸ― π€π‚π€πƒπ„πŒπ˜ ✧✦
June 13, 2025 at 01:19 AM
~ A yanzu Solana kwaya daya (full unit) yana kan farashin Dala 157, idan bani da kudin da zan sayi SOL guda daya zan iya sayan wani bangare nasa kamar 0.5 SOL, 0.02 SOL, haka ma Bitcoin zan iya sayan 0.05 misali, to su NFT ba zaka iya sayan su irin haka ba. Ba zaka iya yankan 0.3 na wani NFT ka saya ba, sai dai ka saya guda (full unit) to shine Non Fungible din, ba'a iya tsaga shi ko fasa shi a sayi wani bangare kamar yadda ake iya sayan 0.1 BNB ko Bitcoin. NFTs suna dauke da digital value na wani abinda yake akwai shi a zahiri, misali "Durov Cap" akwai ta a zahiri amma anyi mata kudi anyi tokenizing dinta Online. Idan ka sayi na Online din kamar exactly ka sayi wancan na zahirin ne. Kuma yana iya kasancewa zallan digital value ne dashi ba lallai ya zama akwai shi a zahiri ba. Kamar Digital Land wanda kamfanin SandBox suka yi NFT dinsu a 2022 kuma suka yi daraja sosai. Duk wani NFT daka gani to shi kadai ne babu irin sa sai dai mai kama dashi amma ba exactly shi ba, misali: ~ Bitcoin akwai irin sa exactly har guda miliyan 21,000,000 babu abinda ya bambanta wani Bitcoin da wani, amma NFT kwaya to kwaya dayan ne kawai, misali: za'a iya yin NFT na Sarkin Kano akan TON blockchain, Sarki Ado Bayero, sannan za'a iya yin NFT na Sarki Aminu ko Sarki Sanusi, kaga waΙ—annan mutane ne daban daban. NFT na farko da aka fara yi Crypto da Blockchain industry shine wanda aka yi proposing akan Ethereum a 2018, proposal din ya fito da EIP-721 daga baya DAO suka amince ya koma ERC-721 kamar dai yadda kowa yasan yadda ake yin proposal akan Ethereum, daga EIP zuwa ERC. Kamar yadda ake da kasuwanni Crypto CEX da DEX to suma haka NFT suke da kasuwannin su. Wanda aka fi sani a duniya itace OpenSea, tana kan blockchain fiye da 20, kamar Bitcoin, Ethereum, BNB, da sauran su. Akwai irin su Getgems akan TON, har wa yau akwai kasuwar Fragment akan TON, akwai Magic Eden da Tensor da Nifty duk akan Solana, akwai XRP Cafe akan XRP chain. ~ Akwai Rarible da Foundation akan Ethereum. Suna nan da yawa gaskiya. Sannan NFT suna da "Rarity" wato yanayin yadda suke a kasuwa, zai iya zama suna da yawa kamar daga 1 zuwa 100 suna bangaren high Rarity, wato basu da yawa. Gwargwadon Ζ™arancin NFT a kasuwa gwargwadon darajar sa, idan suna da yawa zaka ga Rarity dinsa is Common, to ba lallai yayi daraja sosai ba. Idan kuma wani abu ne daban kamar Expensive, Light, ko Legen ko Gifted zai iya yin daraja gwargwadon irin darajar abinda ke kunshe cikin NFT din da kuma darajar da aka bashi tun da farko. A yanzu haka TON ya zarce kowane blockchain wajen daily trade na NFT a duniya, idan akwai wanda ya zarce shi bai wuce Ethereum ba, tun bayan NFT na Gift da Pavel Durov ya raba. Kuma wani abun burgewa shine Telegram Collectibles Gifts ana iya Swapping dinsu Off-Chain. NFT gifts da TON suka yi suna kan wallet guda dubu 184,021 kuma rabin su anyi trade dinsu. Telegram Stars da TON coin da kuma Gift suna daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen motsawar TON blockchain. Sai dai muna ganin Stars din zasu iya kawo tsaikowa TON coin, duk da cewa bamu san tsarin da suka yi ba nan gaba. Ya ake yi NFT yayi daraja? Dayan uku ne: 1. Ko dai abinda aka yi NFT dinsa ya fito daga wani babban mutum mai daraja (kamar Durov Cap 🧒) ko hoton wani Sarki, ko zanen wata masarauta (Fada). 2. Ko saboda tsananin kaunar da mutane suke yi ma wannan abun. 3. Ko kuma saboda ana neman sa ruwa Ajallo domin ayi amfani dashi, wani zai ce kamar yaya? Idan kana yawan buga wasanni "Games" akan Blockchain kuma Games na kudi zaka ga yawancin su NFT ne. Misali: Game din kwallo (Ball), sai kace kai ne Ronaldo, Owen ko Fele, ko Kanu Nwanko, Okocha ko Babangida, sai a baka Ronaldo shi kadai, sai ace kafin ka fara iya buga Ball din sai kayi dressing din Ronaldo, sai ka sayo Rigar Ronaldo, Wandon sa, takalmar sa, Rigar NFT ce zaka je NFT marketplace ka sayo. Wando da takalmar duka NFT ne, zaka je ka biya a baka, sai ka sakawa Ronaldo din, wani zai je ya sayo kayan Okocha ko Ahmad Musa, daga yadda ake zuwa sayan kayan daga nan darajar su ke karuwa. Ina fatan mun gane, idan ka sayi Rigar Ronaldo to ta kare kenan sai dai in an sake yin wata Rigar. So, masu siyar da NFT suna siyarwa masu buga game suna saya. Haka abun yake a bangaren littattafai da sauran su. Haka idan Game din yaki (War) ko fada (Battle) kake bugawa za'a ce ka sayo Bindiga, ko Bullet ko Bullet prove shirt πŸ‘•. Zaka same su ne a kasuwar NFT idan ka sayo sai ka saka kaje kayi yakin. Kada rubutun yayi yawa bari mu tsaya a nan, nan gaba zamu duba yadda ake yin NFT din, da kuma digital identity da verification da suke dauke dashi akan Blockchain, sai rabe raben NFT da kuma yadda zamu amfana da NFT fiye da yadda ada mutane suke kallon NFT a matsayin wani bakon abu ko abin Gwaigwai πŸ₯³ da sauran su. Harka ce mai fadi mai girman gaske, a yanzu a duniyar blockchain babu inda NFT yake yin daraja kamar kan TON blockchain a 'yan watannin nan, saboda me? zamu bayyana haka nan gaba, in sha Allah.

Comments