
Bakandamiya Encyclopaedia
June 5, 2025 at 08:45 PM
Layya ita ce abin da ake yankawa na dabbobin ni'ima (rakumi da shanu da rago da akuya) ranar idin babbar sallah, don neman kusanci ga Allah Maɗaukakin Sarki. Yanka dabbar layya ibada ce mai girma wacce Allah Ya shar’anta ga musulmai. Dalilin shar’ancinta ya zo a cikin Al-ƙur'ani da Hadisai da ijma’in malamai. Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “To ka yi sallah don Ubangijinka, kuma ka soke (dabba)”. Suratul Kausar, aya ta 2. Wasu daga cikin malaman tafsiri sun ce ayar tana nufin: “Wato ka yi sallar idi, kuma ka soke ko ka yanka dabbar layyarka”.
Daga Anas Bin Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Lallai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi layya da raguna guda biyu masu roɗin fari da baƙi, madaidaita ƙaho guda biyu, ya yanka su da hannayensa, yana mai ambaton sunnan Allah, da yin kabbara, ya kuma ɗora ƙafarsa a gefen wuyansu”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito wannan hadisi. Haka nan hadisi ya tabbata daga Ummu Salma (Allah Ya yarda da ita), ta ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Idan kwanaki goma suka shiga, kuma ɗayanku ya so yin layya, to kada ya taɓa wani abu daga gashinsa da fatarsa”. Muslim ne ya rawaito shi.
Domin karanta cikakken bayanin a taɓa link ɗin da ke ƙasa.
👇👇👇
https://bakandamiya.com/hukunce-hukuncen-layya/
👍
9