
TRT Afrika Hausa
June 16, 2025 at 07:45 AM
Baƙin hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar Tel Aviv bayan Iran ta ƙaddamar da munanan hare-haren makamai masu linzami a Isra'ila da sanyin safiyar yau Litinin.
Iran ta ɗauki matakin ne domin yin ramuwar gayya bayan Isra'ila ta kai mata hare-hare ranar Juma'a, inda ta kashe wasu manyan hafsoshin sojinta da masana kimiyyar nukiliya.

👍
❤️
🇮🇷
🇵🇸
😂
🇮🇱
🇹🇯
😢
😮
🙏
57