
TRT Afrika Hausa
June 16, 2025 at 05:48 PM
An dage ziyarar da shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya shirya kai wa jihar Kaduna, inda zai fara ziyartar Jihar Benue da ke fama da rikice-rikicen da suka janyo asarar rayuka da dukiyoyi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga ya fitar ta shafin X a ranar Litinin, an bayyana cewa ziyarar na da manufar yin duban tsakani da neman mafita ga rikicin da ya yi ajalin mutane da dama a Benue.
Sanarwar ta ce a yayin ziyarar, Tinubu zai gana da dukkan masu ruwa da tsaki, - ciki har da shugabannin gargajiya, ‘yan siyasa, shugabannin addini, shugabannin jama’a, da kungiyoyin matasa - don lalubo bakin zaren rikicin da ake samu a jihar da ke yankin tsakiyar Nijeriya.
https://trt.global/afrika-hausa/article/3ed9dabcfc75

👍
😂
🙏
❤️
🇮🇷
🇵🇸
👺
😢
❌
❤
35