TRT Afrika Hausa

TRT Afrika Hausa

53.3K subscribers

Verified Channel
TRT Afrika Hausa
TRT Afrika Hausa
June 17, 2025 at 05:39 PM
Ƙungiyar Agaji ta Red Crescent ta Iran ta fada a jiya litinin cewa uku daga cikin masu aikin cetonta sun mutu sakamakon wani hari da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai a arewa maso yammacin Tehran a lokacin da suke taimaka wa waɗanda suka jikkata. "Wannan lamarin ba wai kawai laifi ne kan dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa ba, har ma da kai hare-hare a kan bil'adama da kyawawan ɗabi'u," in ji kungiyar, inda ta aƙra da cewa ma'aikatan suna taimaka wa waɗanda suka jikkata a gundumar Shahid Bagheri ta Tehran. Wannan dai shi ne aƙalla karo na biyu da Isra'ila ta kai wa ƙungiyar Agaji ta Red Crescent hare-hare. A ranar Asabar ɗin da ta gabata, ƙungiyar ta ce harin da Isra’ila ta kai ya afka kan ɗaya daga cikin motocin ɗaukar marasa lafiya a yankin arewa maso yammacin kasar, inda ya kashe mutane biyu.
Image from TRT Afrika Hausa: Ƙungiyar Agaji ta Red Crescent ta Iran ta fada a jiya litinin cewa uku...
😢 🇮🇷 👍 🇵🇸 😂 🙏 🇳🇬 33

Comments