
TRT Afrika Hausa
June 17, 2025 at 09:14 PM
Golan Manchester United, Andre Onana ya ziyarci shugaban kasar burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore.
Rahotannin sun ce Onana ya je kasar ne don halartar wasannin tara kuɗin jin-kai da gidauniyar Bertrand Traoré Foundation ta shirya.
Da yake miƙa wa shugaba Traore jesi mai dauke da sunansa da sa-hannunsa, Onana wanda ɗan asalin Kamaru ne, ya bayyana godiyarsa kan tarbar da ya samu a ƙasar, ya kuma yaba wa al’adu da al’ummar ƙasar da ke Yammacin Afirka.

👍
❤️
🇵🇸
😂
🙏
♥
❤
🇮🇷
🇹🇷
54