TRT Afrika Hausa

TRT Afrika Hausa

53.3K subscribers

Verified Channel
TRT Afrika Hausa
TRT Afrika Hausa
June 19, 2025 at 03:50 AM
Gwamnatin Nijeriya ta ce tana shirye-shiryen kwashe 'yan ƙasarta da suka maƙala a Iran da Isra'ila saboda yadda yaƙi yake ta'azzara tsakanin ƙasashen biyu. Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokoin Wajen Nijeriya ta fitar ta ce tana dab da kammala shirye-shiryen fara kwaso mutanen da suka makale, don haka ta shawarci 'yan Nijeriya da ke Isra'ila da Iran su tuntuɓi ofisoshin jakadancin Nijeriya a kasashen da suke, don sanin halin da ake ciki. Haka kuma sanarwa ta jaddada kiran a tsagaita wuta nan take a yakin da ƙasashen biyu suke yi da juna.
Image from TRT Afrika Hausa: Gwamnatin Nijeriya ta ce tana shirye-shiryen kwashe 'yan ƙasarta da su...
😂 👍 🇮🇷 🇵🇸 😮 🤣 22

Comments