Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 19, 2025 at 02:43 PM
Ya ku matasa 'yan uwana, wannan muhimmiyar shawara ce gareku mai matukar tsada da bazaku sameta a rumfunan kasuwa ba. Ku ware lokaci ku karanta a tsanake - za ta amfane ku. Muddin kuka karanta da budaddiyar zuciya, zata dasu ta zauna a karkashin zukatan ku, ta amfaneku acan gaba. Ayanzu fa, akasarin mutanen da suke kewaye daku basu damu da ku, ko irin halin da kuke ciki ba. Ballantana kuma makomarku. Lokacin da kuke tsakiyar fafutuka ko kuke fuskantar kalubalen rayuwa, kada kuyi zaton wani, ko wata, ko wasu zasu tsaya muku kukai gaci. Akasari, sai idan matsananciyar "Kasuwar Bukata" da suke hange a tattare da ku. Ku kiyayi bayyana sirrukanku ko matsalolinku da kowa, koma waye. A mafi yawan lokuta bayyanawar bata magance komi. Hasalima, saidai ayi amfani dasu a yake ku acan gaba. Al'ummarmu ta yau ta rasa tausayi, jinkai da alkibla. Ba duk wanda kasani bane zai iya taimaka maka a lokacin matsananciyar bukata. Da yawa sai sun saurari bukatunka da sirrukanka sai suyi kamar basu taba ji ba, suyi biris dakai. Kuma ko a jikinsu. Zasuyi watsi dakai ne saboda baka da wani muhimmanci awajensu. Wasu ma, ba zasu tsaya anan ba, zasuyi maka batanci a bayan idanunka, surinka kiranka da sunaye iri daban-daban. Wani ya dawo gareka, wani kuma jama'a suke kallonka dasu saidai Allah yayi maka sakayya agobe kiyama, laifinka kawai saboda ka nemi ya zamar maka"Tsani" kazama wani. Haka akasarin jama'armu suke ayanzu. Wanda kake ganin zaku iya kashewa ku binne tare, zai iya sanya bakin-bindiga ya harbe ka har lahira. 🟢 MUNA WANI ZAMANI DA TSARIN "JARI-HUJJA" KE TAFIYAR DA KOMI: Idan har ya zamana kafito ne daga gida mai karamin karfi, saidai taka ta fissheka kawai; kayi ta kanka. Jama'a yanzu sunfi taimakon masu hali, su karawa mai-karfi karfi. Idan kana talaka, gani suke babu wani alfanu su taimakeka saboda sunayin taimakon ne da burin samun sakamako acan gaba. Kai kuma gani suke ba zasu samu hakan daga wajenka ba. Ba zasu dauki kiranka ba ko su maida maka martanin sakonka na kar-ta-kwana. Ba zasu agaza ba. Saboda me? Saboda kafito daga gidan talauci. Sun gwammace su taimaki masu hali da farcen-susa, ba don masu halin suna bukatar taimakon ba, a'a. Sai don tsammanin Gobarar-Titi daga wajensu acan gaba. To, idan ka tsinci kanka a irin wannan mawuyacin halin, ka mika al'amuranka ga Allah Madaukakin Sarki. Shi kadai ne zai magance maka damuwarka. Kada ka batawa kanka lokaci wajen neman taimakon bayinsa da basu damu da matsalarka ba - batawa kanka lokaci kawai kake. 🟢 CIKIN MAWUYACIN HALI, ZAKA FAHIMCI MUTANE IRI BIYU: 1. MUTANEN DA KASANI ⬇️ Sune mutanen da suka sanka kasansu amma ba zasu taba taimakonka ba ta kowacce fuska. Sunfi son kullum suji cikinka, su tausaya maka a fuska, su yi maka dariya acan cikin zuciya. A wajensu, taimakonka bata dukiya ne, saboda bakakai ba. Koda kasamu kun hadu zasu nuna maka halin ko-in-kula. Ka kiyayi irin wa'yannan mutane. Zasu bata maka karfi ne da lokaci kawai, daga karshe suyi watsi da kai. 2. MUTANEN DA KAKE DASU ⬇️ Kasancewar ba za'a taru duk azamamWa'yannan sune daidaiku, kadan kwarai acikin al'ummarmu ta yanzu, masu nagarta. Idan matsala ta taso, zasu tsaya tareda kai ba zasu gujeka ba. Zasu damu da irin halin da kake ciki tamkar matsalarsu ce. Zasu taimaka maka ba da manufar samun wani sakamako daga wajenka ba, kawai saboda kauna. Kada kayi wasa da irin wa'yannan mutane. Amma fa sune kaso 1 cikin 100 na al'ummar yanzu. A cikin wani garin ma, ko wata unguwar ba'a samun irinsu ko kwaya daya ! Muna cikin wata irin al'umma me bayyana RIYA da DADIN-BAKI da DADADAN KALAMAI. Zaka kira mutum ko ka tura masa sako, amma atatam zai nuna samsam shi bai gani ba, bai san lokacin ba. Wani abin mamaki da al'ajabi kuma, aduk lokacin da Allah ya kawo maka rufin asiri da tagomashi ba tareda kowacce irin gudunmowarsu ba, su ne zasu fi kowa gudowa zuwa wajenka suna tayaka murna. Suke ikirarin cewa, "Muna matukar alfahari dakai" Ko alfaharin meye, Oho? Kai da kakasa taimakon mutum sadda yakusa mutuwa, yake fadi-tashi, ya akayi kuma kake alfahari dashi ayanzu? Tayaya? Abinda yafi komi ban mamaki ma, har suyi ikirarin ai sune suka agaza maka kakai inda kake a halin yanzu saboda tsantsar rashin kunya da rashin tsoron Allah. Kaki mutum sadda wahala takusa ta hallaka shi, yanzu kuma yakaiga nasara kana ikirarin daukar nauyi. A bayyane yake karara cewar ayanzu akasarin jama'a basuson kaci gaba. Sun gwammace suke ganinka cikin wahala kullum kana gindinsu kanayi musu fadanci, kana tsufa a karkashinsu da 'ya'yansu maimakon ka samu 'yancin dogaro da kanka ta dalilinsu. Basu son su bayarda kowacce gudunmowa da zaka girma ka daukaka saboda babbar barazana a garesu shine ka daukaka. Daukakarka babbar barazana ce a wajensu da iyalansu da yaran gidansu. Wannan shine hakikanin zamanin da muke ciki. Na rantse da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, ayanzu akasarin mutanenmu "JABU" ne marasa inganci. Idan kayi inkarin wa'yannan kalamai nawa, kawai ka jira sadda wata matsala zata taso maka, zaka tuna wannan. A lokacin ne zaka gane hakikanin bambancin dake tsakanin MUTANEN DA KASANI da MUTANEN DA KAKE DASU. 🟢 WANNE SAKO NAKESON ISARWA? Kafita daga sabgar jama'a ka rike Allah wanda ba ya gori kuma baya rowa. Ka tashi kayi aiki tukuru kanemi na kanka, zai baka. Akasarin mutanen yanzu ba kaunarka suke ba. Karya suke ! 🔴 FADAKARWA Duk inda kaga kalmar "TAIMAKO" cikin wannan rubutu nawa, ba yana nufin "Roko" ko "Bara" ko "Maula" ba. Kalmace da nake nufin silar cicciba wani yakai Tudun-muntsira wanda Addini da Al'ada suka halastawa kowanne irin mutum domin ya fito da wata baiwa ko fikira da Allah ya hore masa, ya taimaki kansa har ya taimakawa wasu a rayuwa. Ko kusa, wannan shafi baya karfafa guiwar ROKO ko BARA ko MAULA ta kowacce siga. Alkalamin Auwalu El-Yobawi Bayamari 🖊️ Mai son ganin gobenku ta inganta ! 19-06-2025
👍 🙏 ❤️ 😢 😂 😙 19

Comments