Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 19, 2025 at 04:23 PM
Shawara ga wadanda ke damuwa kan lallai sai sun kasance da wani. Yana da kyau ka sani babu wani Mutum da sai da shi zaka rayu duk girman shaquwarku, soyayyace, abota ce ko mutunci duka suna yiwuwa ne kadai in bangarori biyun sun amince, mutum daya ba ya iya tafiyar da Soyayya ko abota shi kadai, ko hausawa sun ce karfe daya ba ya amo, Uwa ma ta na haihuwa a take ta mutu ta bar jaririn ta, kuma ya rayu cikin yardar Allah. In da gaske tsakani da Allah ka ke tare da mutum wajibi ka fada ma sa gaskia, ka bashi shawara, ka nuna ma sa abinda ya kamata, ka kula da shi ka kuma ba shi kariya. Lokacin da ka fuskanci mutum ya ja baya ko ya na nuna halin ko in kula ko dar-dar da kai, bayan ba haka ka san shi ba, ka yi kokarin binciken dalili, ta hanyar bibiyar sa da bashi damar magana, in ka ga yaqi baka hadin kai, toh ka rabu da shi ya je, ba mamaki iya mu'amalar da ku kayi ta wannan lokacin, ita Allah ya qaddara zata faru a tsakanin ku. Ka girmama kanka, ka fita sabgar wanda ba ya ta taka, kana da 'Yan'uwa, kana da wasu abokan, toh ka yi da me yi da kai, wanda a baya yayi da kai daga baya ya janye sbd wani dalili da ka sani ko ya barwa kansa sani, ko kuma dalilin daukar ziga akanka daga wasu da ke gefe, kar ka da mu, ka bar shi, in dai ba ka zalince shi ba a mu'amalar ku toh Alhamdulillah. Ka da ka zauna garin son sai kay tarayya da wani ka zubar da kimar ka, yanda ya tafi ya bar ka, wani yana nan yana addu'ar qaddara ta kusan tashi da kai, ita dama duniya ta gaji haka mutane wasu na zuwar ma, wasu na tafiya ne, kuma kowa da akwai dalilin da ke kawo shi jikin ka, kai dai ka wanke zuciar ka, ka zauna da kowa lapia. Ka daina damun kanka da lallai sai wani yayi da kai, Bahaushe ma yace in wani ya kika da wuni wani zai so ka da kwana. Ma'assalam.
❤️ 👍 🙏 😢 13

Comments