Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 06:06 AM
Duk wanda zai gija ramin mugunta ya gina daidai shi. Wani miji da matarsa suna rayuwa cikin kwanciyar hankali da farin ciki. Ranar wata Lahadi mijin ya dawo daga wurin aikinsa ya sanar da matarsa cewa ya fara kewar iyayensa da ‘yan’uwansa da 'ya'yansu, kuma ya yanke shawarar gayyatar su zuwa gidansa don su ci abincin tare gobe. Ya roƙe ta da ta dafa masu abinci mai daɗi na alfarma wanda ya dace da darajar iyalinsa. Matarsa ta nuna rashin jin daɗi, ta ce cikin ƙyashi: “In shaa Allah, za a yi.” Ba ta ce komai fiye da haka ba. Mijin bai ɗauki abin da matarsa ta faɗa da mahimmanci ba, sai kawai ya ce da ita: “To, zan kira iyalina in tabbatar musu da gayyatar gobe.” Matar, cikin murmushi mai cike da ƙyashi, sai wata muguwar dabara ta zo mata, ta ce: “To, mai gida, kayi yadda kake so.” Washegari... Da safe, mijin ya tafi aiki kamar yadda ya saba. Da ƙarfe ɗaya na rana ya dawo gida da wuri ya tambayi matarsa: “Meye kika shirya wa iyalina? Zasu iso cikin nan da sa'a guda.” Sai matar ta ce da shi cikin rashin kulawa: “Ban dafa komai ba. Ai iyalinka ba baƙi ba ne, zasu iya cin duk abin da suka samu a cikin gidan.” Mijin ya kalle ta cikin fushi ya ce: “Subhanallah! Yaya za ki ce haka? Ba tun jiya na ce miki iyalina zasu zo cin abinci ba? Kuma nace ki dafa masu abinci mai daɗi.” Yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa gida. Yanzu me kike so in yi? Sai matar ta ce da shi: “Ka kira su kawai ka ce wani aikin gaggawa ya taso maka, su daga ziyarar tasu. Ai ba baƙi ba ne, iyalinka ne.” Mijin ya kalle ta cikin fushi sannan ya fita daga gida ba tare da ya ce wani abu ba. Bayan 'yan mintuna, sai ga shi ana kwankwasa ƙofar gidan. Matar ta tashi a hankali tana tunanin iyayen mijinta ne suka iso, amma sai ta ga iyayenta da ‘yan uwanta ne suka shigo cikin gidan! Ta tsaya cak, baki buɗe, mamaki ya hana ta motsi. Ta tarbe su da ƙyar kuma ta ba su wuri. Suka tambaye ta inda mijinta yake, sai ta ce musu ya fita yanzu-yanzu. Sai mahaifinta ya ce: “A'a, jiya mijinki ne ya gayyace mu zuwa cin abinci, ya ya zai yi gayyata da kansa sai kuma ya fita?” Zuciyar matar ta buga, ta rikice, ta fara shafa hannayenta cikin ruɗani, bata san me zata ce ba balle ta san me zata basu su ci. Abincin da ke cikin gida bai dace da iyayenta ba, kuma ba za ta iya ba su shi ba. Ta kira mijinta cikin fushi: “Me ya sa baka gaya min cewa ka gayyaci iyayena su zo cin abinci ba?” Sai mijin ya amsa yana dariya: “Ai iyalina da naki duk ɗaya ne, ko ba haka kika ce ba jiya?” Matar tayi magana tana roƙon shi: “Don Allah, ka taho mana da abinci daga waje, babu wani abinci a gida da zan iya ba iyayena!” Sai mijin ya ce cikin kwanciyar hankali: “A yanzu dai nayi nesa sosai da gida, kuma ai su iyayenki ba baƙi ba ne. Ki ba su daga cikin abincin da ke gida – kamar yadda kike so ki ba iyalina jiya.” Idan zaka gina ramin mugunta..............?
👍 😂 🙏 ❤️ 😃 🤔 36

Comments