Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 06:52 AM
Idan kayi dace da mace mai irin wannan halayyan ka gode wa Allah................. 1.mace mai tsananin tsoron Allah,sannan tana son ka tsakanin ta da Allah bawai don wani abu naka ba. 2.mace mai hakuri da kawaici akan abu ba komai zata yi magana ba,ba komai zata nuna maka bacin ranta ba. 3.mace mai tsananin ladabi da biyayya mai kokarin faranta maka. 4.Mace mai kunya da kamewa da rike mutuncin ta a duk inda zata je,irin wannan macen baka da fargaba akan ta. 5 .Mace mai kyakkawan lafazi da iya magana,tana kokarin duk maganar da zata gaya maka zata kiyaye. 6.mace mai saukin kai a gare ka, mai jin maganar ka da kulawa da iyayen ka da kuma dangin ka. 7.Mace mai aji da iya kwalliya na aji da iya shigar kamala. 8.Mace mai kyakkawan zuciya,marar kishi na hauka kona hassada. 9.Mace mai addini daga boko har Arabic din sannan tana aiki dashi. 10.Macen da bata yawo tana fita sai da dalili, tana tayaka kishin kanta. Irin wannan macen idan ka same ta karkayi wasa da ita,kayi kokarin ganin ka rike ta da kyau,kar kuma ka cutar da ita domin irin wannan macen basu da yawa a cikin mata. ©️ Nusaiba Tasiu Abdulrahim
❤️ 👍 🙏 😮 😂 34

Comments