
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 07:15 AM
YAN UWANA MAZA INA ZAMUJE DA WANNAN RASHIN KISHIN?
بسم الله الرحمن الرحيم
A gaskiya dayawa cikin mazaje na wannan zamani ko Qamshin Aljannah bazasuji inji Annabi Muhammad صلى الله عليه وسلم
Dalili kuwa shine Annabi yace duk wanda baya kishin iyalinsa (Dayyuth) ko Qamshin Aljannah bazaiji ba
Abun takaici da ban haushi yanzu zaka wani yabar matarsa tafita Babu Hijab babu Niqab ba safar Hannu da kafa wai saidai Gyale kuma gashi tasaka kaya masu matse jiki wani bangaren jikinsu duk a bayyane kamar Wuya da kafarta da damtsen hannunta سبحان الله
Wasu kuma ko ajikinsu baidamu ba matar tayi fita irin yadda takeso wannan yazama kenan ma matarka bace kai kadai
Domin indan kasan Qima da darajarta a matsayin ta na matarka wacce kasha wahala kafin ka mallaketa Bazataba taba yadda tafita da shigar da wani zai kalleta a waje ta burgeshi sbd nuna tsiraicin ta ba
Indai kai mutumin kirki ne mai kishi kuma wanda yasan Qima da darajar 'ya mace yakeson samun Rahamar ubangijinsa toh bazabar matarka tafiba sai ka tabbatar tayi shiga ta mutunci Hijab har kasa da Niqab Safar hannu da Kafa domin ta rufe wannan surar jikin da ALLAH ya halattamaka kai kadai zaka gani kuma taja hankalinka da ita
Mace idan kana nuna kishi akanta kanunamata tanada darajar da amatsyinta na matarka bakaso komai ya rabeta toh tabbas zatafi kulamata da kanta abangaren kishi da kllacemaka kanta
Matarka matarkace kai dayanka ba matar abokanka bace amma wani shi sbd sakarci sai yanunawa abokansa cewa matarsa tanada kyau Wallahi kai babban sakare kuma bakada kishi Kaida Aljannah ko Qamshinta bazaka ji ba
AYI HAKURI YAU RUBUTUN YA DANYI TSAURI DA KAUSASAWA KO WLH ABUNNE AKWAI TAKAICI
ALLAH yasa yan uwa maza sugane matansu Qimarsu ce kuma mutuncinsu ne
ALLAH YASA MUDACE
Abu Ja'afar Assunny ✍️
👍
❤️
🙏
❤
😮
28