Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 07:22 AM
Diabetes (Ciwon sugar) Ciwon sugar na daga cikin ciwokan da ke wahalar da mai ita, kuma tana da ka'idojin da in anbi za'a rage yawan tashin ta da kuma complications din ta. Ciwon sugar yana faruwa in jiki bai amfana da Sugar dake cikin jini da kuma rashin isheshshen insulin. Insulin shi ke sa jiki ya amfana da sugar ko kuma ya storing din shi (sugar). Ciwon sugar kala biyu ne zuwa hudu. Akwai type1, type2, prediabetes san nan akwai na masu ciki.. Alamomin ciwon sugar sun hada da: 🛑 Yawan fitsari akai akai. 🛑 Yawan jin yunwa sosai sosai kuma akai akai. 🛑 Yawan jin kishin ruwa akai akai. 🛑 Yawan gajiya 🛑 Rashin warkewan ciwo da wuri. 🛑 Yawan rama a type 1 🛑 Gani duru duru. Abubuwan da ke iya(risk factors) kawo ciwon sugar 👉 Overweight , musanman masu tumbi. 👉 Rashi motsa jiki 👉 masu shekaru sama da 45years 👉 Iyaye ko yan'uwa Masu ciwon sugar. Dsss In har a ka gwada mutum sau daya sau biyu aka tabbatar yana da ciwon sugar dole ya kula da abubuwa kaman haka: ✅ Diet = Dole ya rage cin abinci mai starch da carbohydrate sosai, Ya yawai ta cin Kayan ganye, fibre rich food, protein and healthy fat dss= ya nemi shawaran Likita da Dieticians don sanin abubuwan da ya kamata yaci.. ✅ Exercise yawan motsa jiki. ✅ Bin kaidar shan magani. ✅ Gwaji akai akai.. So samu mutum ya mallaki abun gwaji nashi. ✅ Barin Shan Cigari da Giya. In aka kula sosai mutum zai rayu cikin aminci ba tare da yawan tashin hankali ba. Bin kaidojin yana da amfani sosai.... Ciwo neh da mutum zai rayu dashi (type1) iya rayuwarshi.. Saboda haka dole ka yarda da hakan kuma ka bi kaidojin don rayuwa cikin aminci. Dole mu ka re kan mu iya yin mu. Da lafiya ake komai.. Lafiyar ita ce uwar jiki.. Kar ka yarda asa maka ruwa(iv fluid) ba tare da sanin sugar level dinka ba musan man ya shekara 45yrs yayi sama. Sanya ruwan da ake yi gaba gadi ba tare da sanin Sugar status din su ba ya kashe mutane da yawa. Nr. Imrana Shuaibu Adam © Malamin Jinya
🙏 ❤️ 👍 😢 17

Comments