
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 07:30 AM
GYARA JIKI GA MATA
fatan ta yi laushi da sheki:
🌿man zaitun
🌿lalle
🌿kur-kur
🌿 madara peak
Zaki hade wadannan kayan hadin guri daya, sai ki kwaba su ki shafe jikinki da fuskarki, zakiyi wannan hadin kafin ki shiga wanka. Idan ya bushe a jikinki sai ki murje sannan sai ki shiga wanka jiki yana yin kyau yayi sheki
GYARA JIKI 2:
Wannan hadin shi akecewa kafi TURGEWA:
🌿kur-kur
🍶dulka
🍯 zuma
🌿 kwai
🍋lemun tsami
Ki hade su guri daya ki samu ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma yafi kwabin lalle ruwa, sai ki shafe fuskarki
Idan kuma har dajiki kikeso, sai ki shafa harda jiki
Bayan (1hr) sai ki shiga wanka zaki ga yadda jikinki zai goge
GYARA JIKI 3:
( fata ta yi laushi da sheki):
🌿lalle
🌿kwaiduwar kwai guda 3
🌿 manja cokali 3
🌿 kur-kur
Sai ki kwaba su guri daya ki shafe jikinki zuwa (1hr) daya, sai ki yi wanka da ruwan zalla da ruwan dumi ki shafe jikinki da ita sai ki kuma yin wanka
KYAN FUSKA:
Sai ki hade su guri daya ki kirba su cikin turmi, ki mulmula ki rinka wanke fuska zaki ga yadda fuskar ki zatayi.
1.dettol
2.sabulun Ghana
3.garin zogale
4.farar albasa
GYARA FUSKA:
Wanna hadin wanda ya kesa fuska tayi haske da annuri takun Kore kurajen fuska
* bawon kankana
A samu bawon kankana sai a rinka goge fuska da shi yana gyara fuska tayi sumul
GYARA FATA:
1.Lemun tsami
2.bawon kwai
3.kur-kur
Zaki hade su guri daya ki daka su sai ki rinka wanka dashi fatar mace zata goge tayi kyawun gaske
GYARA FATA:
1.ganye magarya
2. sabulun salo
Zaki daka ganyan magarya sai ki zuba a cikin sabulun salo ki rinka wanka yana gyara jiki
GYARA FATA:
*ganyan magarya
*man zaitun
*man habbatussauda
Ana daka ganyan magarya a zuba cikin man zaitun da man habbatussauda shi ma yana gyaran.
GYARA FATA:
🌱 lalle
🍁 garin ridi
Ana amfani da lalle kafin ki shiga wanka sai ki kwaba ki zuba garin ridi ki shafe jikinki zuwa (1) hr sai kiyi wanka.
GYARA GASHI:
Man zogale
Man kwakwa
Man zaitun
Zaki hade su guri daya ki rinka shafawa a kanki
GYARA GASHI:
Man zogale
Ganyan magarya
Kanunfari kadan
Sai ki hade su guri daya ki rinka shafawa a kanki yana sanya tsayin gashi ya kuma yi laushi.
GYARA KAFA:
Baki ba zuwa wajen wanke kafa madarar kinyi amfani da wannan hadin.
🍀 man shanu
🍀 man kwakwa
🍀 man ridi
🍀 man alayyadi
Idan kafa tana tsagewa ko tana kaushi da daddare zaki hada wadannan mayamayen guri daya ki shafa a kafa in zaki kwanta bacci daddare sai ki daure da Leda da safe ki wanke da ruwan dumi ki shafa man zaitun da man ridi
👍
❤️
🙏
😮
❤
😂
24