
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 07:31 AM
Kana miji kuma jagora amma
☆ Baka iya bama iyalan ka kulawa alhali kana da hali da daman yi.
☆ Kullum cikin hantara, fada da tsawa kake mata.
☆ Gyara in za ka mata sai ka haɗa da munanan kalamai dan ka tozarta zuciyarta.
☆ Kullum baka da lokacinta balle ku ɗebema juna kewa cikin nishaɗi, ko kasan damuwarta, amma kana iya kwatankwacin haka da matan banza.
☆ Kalamai, Kulawa da lokacin da baka mata ko bata su kake ma matan da basu chanchanta ba.
☆ Kullum cikin chatting da video call na batsa ka ke da matan banza
☆ Kullum cikin Kwashe kwashen mata kamar kwarkwasa
Da irin wannan halaye ta ina nagartan ka yake ?
Da irin wannan halaye ta ina yake nuna halin miji nagari da mace zataji dadin zama dashi ?
Da irin wannan mu'amala ta ina ka zama jagora da mace zatayi alfahari da shi ?
Ka sani matuqar ka siffantu da aikata wasu halaye daga cikin wannan ko dukan su tabbas matsalar ba matar ka bace kai ne, domin ba matar da zata zauna lafiya da miji mai halaye irin haka.
✍️ Fatimah Chikaire
👍
😢
🙏
❤️
☕
👏
😂
😮
🥰
31