Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 08:11 AM
Wani mutum ya tambayi mai kula da gidan marasa galihu: "Wadanne irin takardu ake buƙata idan ina son na nema wa mahaifina gurbi a gidan marasa galihu?" Sai shugaban gidan ya bashi amsa da cewa: "Takardun da ake buƙata sun haɗa da: 1️⃣ Hoton mahaifinka lokacin da ya dauki mahaifiyarka yana gudu don ya kai ta asibiti lokacin da za ta haife ka. 2️⃣ Hoton shi lokacin da ya ɗauke ka a ranar haihuwarka cikin farin ciki, yana karanta kiran Sallah a cikin kunnenka. 3️⃣ Hoton shi lokacin da yake dawowa daga wajen aikin a wahale domin neman abincin da zai ciyar da kai da sauran duka ‘yan gidan. 4️⃣ Hoton shi lokacin daya ɗaukeka kana zazzabi cikin dare, yana gudu don ya kai ka zuwa asibiti a lokacin sanyi. 5️⃣ Hoton shi yana zaune kusa da makwancin ka bayan dawowar ku daga asibiti, yana ɗora hannunsa a goshinka lokaci bayan lokaci don ya tabbatar da kana cikin koshin lafiya. 6️⃣ Hoton shi lokacin da yake jure wahalar rayuwa da azabar aiki domin ka girma ka tsaya da kafafunka, ka zama mutum mai daraja. 7️⃣ Hoton shi wata guda kafin sallah, yana tunanin yadda zai siyo maka sabon tufafin sallah domin ya ga farin ciki a cikin idonunka. 8️⃣ Hoton shi lokacin daya Keɓance yana share hawayensa da gumi kafin ya shiga gida, domin kada kowa ya gane yana cikin damuwa. 9️⃣ Hoton shi lokacin da yaka karbar aron kudi domin ya biya maka kudin makaranta, ko ya siyo maka waya domin ka rika magana da abokanka — duk da cewa yana cikin mutanen da baza kana kiran shi da wayar akai-akai ba. 🔟 Hoto na ƙarshe: shine lokacin da yake kokarin tara kudi don ya shirya maka bikin aure, yana burin ya ganka ka zama uba kamar shi. Sai shugaban gidan ya ƙara da cewa: "Ya kai ɗana… Lokacin da kake ƙarami, kai ne rayuwarsa gaba ɗaya. Yanzu da ya tsufa… ya zama dole ka rama bashin abinda yayi maka. Shin ba ka taɓa karanta wannan ayar ba daga cikin Al-Qur’ani: ﴿ إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِندَكَ الْكِبَرَ ﴾ [Suratul Isra’i: 23] Shin ya taɓa tunanin kai ka gidan marayu lokacin da kake ƙarami? To, me ya sa kai zaka yi tunanin kai shi gidan marasa galihu yanzu da ya tsufa? Allah ya tsawaita rayuwar iyayenmu, ya jikan waɗanda suka riga mu gidan gaskiya. { وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا }
😢 👍 😭 🙏 🥹 ❤️ 💔 💞 🤲 42

Comments