Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 08:19 AM
HATSARIN DAKE TATTARE DA "BIYAYYA" IDAN AKA MAKANCE A CIKINTA Rubutawa: Auwalu El-Yobawi Bayamari 20-06-2025 Dukda yake sanannen abu ne cewar BIYAYYA kyakkyawar dabi'a ce mai tushe da asali tun talen-tale, da take wakana tsakanin ➡️ Bawa da Mahaliccinsa; ➡️ Iyaye da 'ya'yansu; ➡️ Ma'aurata - Mata da Mijinta; ➡️ Yayye da Kanne; da ➡️ Iyayen-Gida da Yaran-Gida Wanda a dalilin hakan, idan aka samu kyakkyawar BIYAYYA da aka assasa bisa tsari wacce: 👉 Babu wuce gona da iri; 👉 Babu makanta; 👉 Babu biyayya irinta makaho da dan jagora; 👉 Babu ha'inci; 👉 Babu zakewa; 👉 Babu sabawa dokokin Allah da Shari'a; 👉 Babu kin nunawa ubangida gaskiya a hikimance. To sai kaga an samu kyakkyawan tsarin wakilci da gudanarwa, taimakekeniya wajen yiwa al'umma hidima, tsare amana da karfafa yarda tsakanin al'umma. Shi wanda ake yiwa biyayya ya samu natsuwa daga wanda yakeyi masa biyayya, ya rage masa dawainiya, ya taimaka masa wajen gudanar da al'amurra cikin kasaita da isa. A dayan bangaren kuma, wanda yakeyin biyayyar yasamu kyakkyawan jagoranci, nuni, riko da hannaye, ginuwa da cigaba. Tayadda gobensa zatafi yau dinsa kyau daga wajen wanda yake yiwa biyayya. A takaice dai hannun dama ya cuda na-hagu. Anan, bari na mayar da hankali akan biyayyar tsakanin Iyayen-Gida da Yaran-Gida saboda ita tafi yiwa jama'a mummunar illa idan aka samu akasi. Kenan dai, asali, biyayya abu ce mai kyau muddin ba ana yinta bane a makance. Amma fa... BIYAYYA tana tattare da mummunar illa da hatsari kwarai da kololuwar cibaya muddin aka makance a cikinta, aka gaza bayyanawa wanda ake yiwa biyayya gaskiya da abinda ya kamata a cikinta, aka zake a cikinta, sannan ake sabawa Allah a cikinta don agyara miya. GA KADAN DAGA CIKIN ILLOLI DA HATSARIN TA: 1. Fifita al'amurran wani fiyeda na karan-kai, wanda hakan yakesa mutum ya manta da kansa bakidaya ya shagala da hidimar wani, idan bai ankara da wuri ba har karshen rayuwa; 2. Tarnaki daga amfanuwa daga baiwar wasu, rasa sabbin basirori, asarar huldodi ko haduwa da sabbin mutane ko damammaki; 3. Takura-kai da hakurin dole akan abubuwan da basu dace ba; 4. Kazamar alaka. Ta yadda anaji ana gani za'a aikata ba-daidai kawai domin a faranta wa wanda ake yiwa biyayya. Rai a bace amma dole ayi; 5. Gaza sanya shamaki ko iyaka domin tsira da mutunci. Hakan yana maida mutum yazama arahar-banza dukda dimbin daraja irinta Dan-Adam; 6. Wuce gona da iri cikin mafi yawan al'amura wanda hakan ke gogawa mutum mummunan bakinjini a idanun al'umma; 7. Dakon gaaba da fushi da fushin wani; 8. Kololuwar son kai da fifita na-jiki a inda ba'a cancanta ba; 9. Raina sauran mutanen dalilin fifita wanda ake yiwa biyayya ake ganin yafi kowa; 10. Dakon zunubi dalilin daurewa karya gindi da shaidar zur; 11. Rashin cikakken 'yanci da bautarwa. Da idanunka barobaro amma ka zama makaho, da kunnuwanka falofalo amma ka zama kurma; da 12. Barazanar zama "Kawali" idan aka yi rashin sa'a ubangida ko wanda ake yiwa biyayya "Fasiki" ne; Wa'yannan fa kadan ne daga illolin makauniyar biyayya. Girman mummunan tasirin makauniyar biyayya ga sauran daidaikun al'umma ba zasu kirgu ba. Kadan daga ciki: i. Boye wa jama'a gaskiya da rurrufe musu hakikanin al'amari; ii. Karfafa guiwar zalunci idan wakilci ko jagoranci ya gitta; iii. Karfafa kiyayya da gaaba; iv. Rarrabuwar kawuna; v. Macewar zukata da takaita gina-kai; vi. Dawwamar danniya da karfa-karfa. Duk wa'yannan illolin ba kowa yake lura da su ba amma suna yin naso suna kashe dimbin al'umma ahankali ahankali, a tsaye. Dalili kuwa shine ga zahirin mafita amma ba za'a iya fitowa a bayyana ba da sunan biyayya. Daga karshe dai, abin yana barewa ne akan shi wanda yakeyin biyayyar idan tafiya tayi nisa cikin dayan-uku: 1. Ko dai ya amfana da makauniyar biyayyar yasamu duk abinda yakeso amma yayi mummunan karshe; 2. Ko kuma ya fahimci cewar batawa kansa lokaci yayi wajen gina rayuwar wani yana rusa tashi, ya tsani kansa da kansa bayan shekaru sun ja; 3. Ko kuma a rabu baran-baran dutse a hannun riga da ubangida, duniya taji tsakaninsu domin Sunnar rayuwa ce cewar: Duk lokacin da aka samu mummunar alaka tsakanin wasu jama'a ba bisa cancanta ba, daga karshe sai an gansu a rana anyi musu dariya. Bayaga tarin zunubi. WANE SAKO NAKESON ISARWA? ⬇️ Ayi tsabtatacciyar biyayya. Duk biyayyar da zata haddasa koma baya, sabon Allah, daurewa karya gindi, da sabawa Allah a hakura da ita duk abinda ake ganin za'a samu. Ba za'a dawwama a doron kasa ba. Akwai tsufa tun kafin mutuwa. Akwai sauyi da jarrabawar rayuwa. Ba zaka yi makauniyar biyayya kaci banza ba tun anan Duniya duk abinda kasamu a cikinta. Dole saika kwashi kunya da nadama daga karshe, sannan kaje lahira ka amsa tambayoyin daurewa karya gindi da cutar da dubban al'umma a fakaice. Babu inda akafi daurewa karya gindi kamar acikin Makauniyar Biyayya. 🔴 Duk biyayyar da zata hana ka bayyana kuskure domin ya gyara, ko katafi akan kuskure alhalin kana ganin daidai, ko kirikiri abaka umurni mai cikeda ta'adi da datti, kana sane sarai amma kabi umurnin, to wannan biyayyar ta mayar dakai "BAWA". Ta mayar dakai DABBA-DABBA. Da wuya kayi kyakkyawan karshe.
👍 🙏 ❤️ 🕋 😢 👏 😂 😇 😮 84

Comments