Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 10:41 AM
Can a woman satisfy her husband 100%? Wani lokaci mace tana jin kamar idan ta biya wa mijinta bukatu, yi masa girki kala-kala, gyara jiki, , ta tsaftace, girmamawa, ladabj biyayya, kwantar da kai… to zata iya gamsar da shi shalelen 100%. Sai dai gaskiya daya ce Mace ba za ta iya cika dukkan burin mijinta ba, kamar yadda shima ba zai iya cika nataba. Why? Saboda dan Adam bashi da iyaka a bukata. Yau yana son shiru, gobe yana son hira. Yau yana son tuwo, gobe yana son noodles. Yau yana so ki zauna da shi sosai, gobe yana buƙatar sarari. Yau yana so ki yi masa magana da tausayi, gobe yana fushi saboda wani abu da ba ki yi ba. Zuciyar mutum tana canzawa. Rayuwa tana da nauyi. To me mace zata iya yi? – Ki yi niyyar kyautatawa saboda Allah, ba don yawan yabo ba. – Ki fahimci cewa mijinki ba kullum yana buƙatar abu iri ɗaya ba, yau soyayya, gobe space. – Ki gina kawanki da basira ki dinga karanta sauyin yanayinsa. – Ki yawaita addu’a sosai. Saboda ko kina da niyyar gamsar da shi, idan Allah bai sa ki gane hanyar ba, zai zama kamar ba kya yi. Mace mai basira ba wadda ta iya komai bace... Ita ce wadda ta san iyakokinta, amma tana kokari da zuciya daya. Ita ce wadda ta mayar da gida masaukin salama, ko da mijin yana da tabo. Shin zai yiwu ki cika shi 100%? A'a. But you can make him FEEL like he's 100% loved, 100% respected, 100% at peace. Kuma hakan yana da girma fiye da kamalalliyar mace. Kuma ku mazan… Ku fahimci cewa mata na kokari. Idan tana da himma, tana ƙoƙari, tana daraja ka, to kada ka dinga ganin ƙurucinta ko kuskurenta a matsayin gazawa. Girmama ƙoƙari shine soyayya. A ƙarshe You can't be a perfect wife. But you can be a real, intentional, prayerful woman, and that is even more powerful. #fatimakanouniquemarketplace HIJABI QUEENS.
❤️ 🙏 👍 17

Comments