
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 10:41 AM
YOUR DIGNITY IS YOUR CROWN , DON’T HANG IT ONLINE FOR LIKES
Budurwa mai hankali, ki sani cewa social media ba rayuwa bace gaba ɗaya wani ɗan bangare ne ne kawai, kuma yawanci kowa yana nuna abinda zai iyane ba gaskiyar zuciyarsu ba.
Ki kame kanki. Kar ki bi shahara da son yabo har ki manta darajarki. Kadan ne likes ke kawo girmamawa, amma self-respect yana kawo natsuwa da daraja har a duniya har a gaban Allah.
Kar ki zubar da mutuncinki saboda wani challenge.
Kar ki nuna jikinki don kawai ki ja hankali.
Kada ki bayyana sirrinki ko soyayyarki a idon duniya, domin ba kowa ke murna da farin ciki ba.
The way you present yourself is the way the world will value you. If you act cheap, you’ll be treated cheap. If you carry yourself with grace, you’ll be respected.
Ki kasance mace mai aji mai hikima, mai nutsuwa. Kyakkyawa amma ba fuskarka ba a hali da tarbiyya da yadda kike amfani da kafafen sada zumunta.
Mutunci yana da nauyi, kada ki bari wani comment ko DM ya dauke miki shi. Ki kasance budurwa da ke burgewa ba da hotuna ba, sai da ilmantarwa tausasawa, da halin kirki.
Kada ki dinga fasa darajarki saboda ‘followers’, domin Allah yana ganin me kike boyewa da me kike nunawa.
Be proud of who you are, and never let social media define your worth.
Mutuncinki shine ado mafi tsada.
#fatimakanouniquemarketplace
HIJABI QUEENS
👍
❤️
🙏
❤
💯
🤗
🤣
🤭
50