Sirrin rike miji
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 11:17 AM
soyayya tana bukatar hakuri, uzuri, fahimta da sadaukarwa Ukty Idan kika samu masoyi wanda yake sonki saboda Allah, yana ganin ƙimarki, yana kula dake ki rike shi hannu bibbiyu Ki rike shi da addu’a, da kulawa, da soyayyar gaskiya🥰 Masoyi mai hakuri, mai fahimta, mai yawan yafiya, ba kasafai ake samunsa ba. Idan kika samu irin wannan, kada ki yi wasa da zuciyarsa.❤️ Ki kasance masa abar natsuwa, abar kwanciyar hankali, ki zame masa gaskiyar mafarkinsa Koda bakwa tare, ki tabbatar yana jin kamar kina kusa dashi Ki cika rayuwarsa da farinciki da kulawa da murmushinki Ki mamaye zuciyarsa da tsarkakkiyar soyayya❤️ Masoyi na gaskiya rahama ne daga Allah, kyauta ce da ba kowa ke samu ba. Kada ki masa butulci Kada ki bar zuciyarki ta yi wasa da wanda ya ɗauke ki da muhimmanci Soyayya tsarkakakkiya tana samuwa daga addu’a da kulawa, kar ki yi sakaci da abin da wasu ke roƙon Ubangiji kullum amma basu samu ba Ki nutsu, ki nuna masa tsarkakkiyar soyayya. Ki mamaye zuciyarsa har ya dinga jin sautinki koda bakwa kusa da juna yana jin farin cikin da ke ke haifarwa a ransa.🤍 Ki zama abar alfahari a rayuwarsa, kuma ki nuna masa cewa zabinsa bai tafka kuskure ba. Wanda ya ɗauke ki kamar duniyarsa to kicika masa duniyar sa da farinciki 🥰 sannan ko baki tura masa sms ya kasance kina tura masa na Friday dauke da soyayya da addu'a yana tasiri sosai azuciyar masoya 🥰 Misali....... Amincin Allah ya tabbata gareka 🤍 Yau Jumma’a ce — rana mai albarka da rahama. Ina roƙon Allah Ya albarkace ka, Ya buɗe maka kofofin nasara, Ya tsare ka daga sharrin duniya da lahira. Ya sanya farin ciki cikin zuciyarka kuma Ya raya rayuwarka da kwanciyar hankali da natsuwa. Ka kasance cikin kariya da rahamar Ubangiji yau da kullum. Masoyi ka kasance cikin adduana a kullum ❤️ Allah ya saka maka da alkhaeri, Ya azurta ka fiye da tsammaninka. Ina matuƙar kaunarka, kuma ina fatan soyayyarmu zata kai ga madawwamin farin ciki insha ALLAH ♥️ Phateemarh Zahrah ✍️
❤️ 👍 🙏 🥰 😍 🤍 🤣 71

Comments