
Sirrin rike miji
June 20, 2025 at 02:08 PM
Kyautatawa Iyaye Shine Sirrin Samun duk Wani Cigaba a Duniya da Lahira.
A zamanin da, a wani gari, anyi wani tsoho da yake zaune tare da ‘ya’yansa maza guda uku. Tsohon ya kamu da wani mummunan ciwo, wahala da zafin ciwonsa suka kara yin tsanani, amma ‘ya’yansa suka ki kula da shi. Sai ƙaramin ɗansa ne kawai ya nace cewa zai dauke shi ya kai shi gidansa don ya kula da shi kamar yadda mahaifinsa ya rene shi a lokacin ƙuruciyarsa. Ƙaramin ɗan ya roƙi ‘yan uwansa su bar shi ya kai mahaifinsu gidansa, domin shi da matarsa suna kula da shi.
Amma ‘yan uwansa suka ƙi amincewa da hakan, saboda suna tsoron kada mahaifinsu ya rubuta wasiyya ya bar masa dukiyar sa gaba daya, ya bar su babu komai. Lokacin mutuwar tsohon yana kara kusantowa, kuma ga tsufa da ciwo da yake fama dashi sosai.
Daga ƙarshe sai ‘yan uwansa suka yarda bayan sunyi yarjejeniya akan cewa ƙaramin ɗan zai yafe musu gadonsa gaba daya, yace musu shi baya son komai, abinda yake bukata kawai shine mahaifinsa ya zauna tare da shi don ya kula da shi. Daga nan ne suka yarda, saboda ya yi watsi da haƙƙinsa na gado.
Karamin ɗan ya ɗauki mahaifinsa zuwa gidansa, suka dinga kula dashi tare da matarsa, har lokacin mutuwa yayi ya rasu. Bayan wani dan lokaci da rasuwar mahaifinsu, sai ya shiga cikin yanayin talauci sosai, bai da abin da zai ciyar da ‘ya’yansa, kuma ‘yan uwansa ba su ba shi ko sisin kwabo daga cikin gadon ba, duk da cewa ya bar musu ne saboda kulawa da larurar mahaifinsu. Wata rana ya kwanta cikin baƙin ciki saboda babu, sai ya yi mafarkin mahaifinsa yana gaya masa cewa ya ɓoye wata taska a wani wuri, ya tafi ya ɗauka.
Washe gari da safe, sai ya tashi ya tafi wurin da mahaifinsa ya gaya masa a mafarki. A can ya samu akwatin da ke cike da kayan ado masu daraja da zinare mai yawa. Ya yi murna matuƙa, ya tafi wurin ‘yan uwansa ya ba su labarin abin da ya faru. Amma sai suka ɗaga masa murya suna cewa: "Ka riga ka bar mana gadon mahaifinka da hannunka, wannan dukiyar ba taka bace!" Suka kwace komai daga hannunsa.
Washegari ya sake yin mafarkin mahaifinsa yana gaya masa game da wata sabuwar akwatin zinaren. Ya tafi ya gaya wa ‘yan uwansa, suka tafi suka ɗauki akwatin suka ƙi ba shi komai. Ya koma gida cikin baƙin ciki domin bashi da abinda zai ciyar da ‘ya’yansa.
A daren wannan rana, ya sake ganin mahaifinsa a mafarki yana gaya masa cewa ya saka dinare guda daya a cikin tulun ruwan da ke gonarsu. Ya tafi ya gaya wa ‘yan uwansa, sai suka yi masa dariya suna cewa: "Dinare guda daya kawai? Ka ɗauke shi, wannan shi ne gadon da mahaifinka ya bar maka, wawa!"
Ya tafi gonar ya ɗauki dinaren, domin yana cikin tsananin buƙata sosai. Yana kan hanyar dawowa sai ya ci karo da wani tsoho zai siyar da kifaye biyu da ya kamo daga tabki. Tsohon ya ce: "Ka ɗauki waɗannan kifayen ka bani dinare ɗaya." Ya yi murna sosai domin babu abin da ya rage masa sai wannan dinare ɗaya. Ya tafi gida da kifayen cikin farin ciki, yana murna don ya samu abinda zai iya ciyar da ‘ya’yansa. Ya gode wa Allah, ya yi wa mahaifinsa addu’a bisa wannan dinare da ya bar masa.
Yayin da matarsa ke yanka kifin farko, sai ta tarar da wani babban dutse mai daraja a cikinsa. Ta yanka kifi na biyu, sai ta sake tarar da wani dutsen wanda yafi na farko girma. Duwatsu ne na musamman wanda ba kowa ne ya taba ganin irin su ba, haka ya sa suka zama abin magana a cikin gari. Sarki ya ji labarin su, kuma ya nuna yana son duwatsun masu daraja, sai ya karɓe su daga hannunsa ya ba shi kuɗi masu yawa. Karamin ɗan ya zama mai arziki, ya ci gaba da rayuwa cikin farin ciki yana yi wa mahaifinsa addu’a.
“Ya Allah, Ka ji ƙan iyayenmu, Ka gafarta musu, Ka sa mu zama masu biyayya a gare su.”
❤️
👍
🙏
❤
13